Daga Isa Ahmad Getso
Kira don nemawa Barr. Ibrahim Isa Aliyu (Matawallen Gwagwarwa) makoma a gwamnatinka
Ya Mai Girma Gwamna Abba Kabir Yusuf
Na rubuta wannan wasiƙar a matsayina na ɗan ƙasa kuma Wanda yake ba da gudunmawa wajen ci gaban dimokuradiyyar jiharmu ta Kano.

A tsawon lokacin da ka dauka kana fafutukar neman gwamnan Kano har ka yi nasarar shiga ofis, daidaikun mutane da dama sun tsaya tsayin daka a wajenka ganin ka Sami wannan nasarar kuma daga wadancan yan kishin Kasar a cikinsu har da BARR. Ibrahim Isah Aliyu, wanda aka fi sani da MATAWALLEN GWAGWARWA.
Wannan matashin ya bayar da gudunmawa da karfinsa, basirarsa, da dukiyarsa wajen yakin neman zabe kuma bai yi haka don amfanin kansa ba, sai don Samar da shugabanci na gari a jiharmu. Ya tattara goyon baya, don ganin sun zabe ka sun kuma Kare kuri’un da yin duk abun da ya kamata .
Bukatun Nigeria da Tinubu ya mika a taron da ake yi a Japan
Amma duk da Wannan kokarin da Barr. Ibrahim Isa ya yi har yanzu ba wani abu da aka yi masa da yake nuna yabawa bisa kokarin da yayi don kafuwar Wannan gwamnati. Rashin ba shi dama a wannan gwamnatin ya jefa matasa da dama cikin damuwa .
Ba mu rubuta wannan wasiƙar don neman gwamnan Kano ya yabawa wadanda suka ba shi gudunmawa, Muna tunasar da gwamnan cewa Idan aka yi watsi da masoya irin su Matawallen Gwagwarwa, hakan yana Sagar da gwiwar masoya . Amma idan aka karrama su aka yabawa musu hakan yana kara dankon soyayya tsakanin gwamnati da wadanda ake mulka.
Don haka muna kira ga gwamnatin Abba Kabir Yusuf da ta duba gudunmawar da Barr. Ibrahim Isa Aliyu da makamantansa su ka bayar. Tabbas yin hakan zai karawa magoya bayan kwarin gwaiwar cigaba da ba da gudunmawa.
Tare da matuƙar girmamawa,
Comr. Nasir Danjuma Gwagwarwa
Daga kungiyar Muryar al’umma tun daga Tushen Tushen
Jihar Kano.