Kwankwansiyya Singa Market ta yabawa Salisu Takai bisa samawa Matasan Kano aiyukan yi

Date:

Daga Ibrahim Sani Gama

 

Kungiyar kwankwasiyya singa market ta yabawa matashin Dankasuwannan Alh.Salisu Biliyamunu Takai bisa yadda ya ke taimakawa wajen daukar matasa ayyukan yi domin dakile masu fadan daba da shaye-shayen muggwan kwayoyi a fadin jihar Kano.

Jama’in yada labarai na Kungiyar Abubakar Abdullahi Kanavaro ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da Manama labarai a nan Kano.

FB IMG 1753738820016
Talla

Abubakar Abdullahi Kanabaro ya ce Buliyaminu Takai mutum ne da yake damuwa da al’amuran matasa domin su samu damar dogara da kawunansu Inda yace,watsi da wadan nan matasa na daya daga cikin abubuwan da suka sanyasu Shiga wasu munanan dabi’u na kwacen wayoyin alumna da shaye shayen muggwan kwayoyi.

Ya ce lokaci yayi da Gwamnatin za ta tallafawa matasa domin dakatar da su wajen aikata munanan dabi’u da suka danganci kwacen wayoyin alumma Shan miyagun kwayoyi,amma yace dole iyaye su sanya idanu Kan ‘ya’yansu domin sanin irin ayyukan da suke yi a rayuwarsu ta yau da kullum.

Magoya bayan NNPP Kwankwansiyya a Bagwai na neman agajin Gwamnan Kano da Dungurawa

Kanavaro ya ce kungiyar kwankwasiyya singa market tana zakulo irin wadan nan matasa yankasuwa irinsu Alh.salisu Buliyaminu Takai domin yaba musu akan gudunmawar da suke baiwa matasa a fadin jihar Kano.

Ya ce suna yin hakan ne domin karawa sauran al’umma karsashi wajen Jan matasa a jikinsu da wayar musu da Kai domin barin munanan dabi’u da suke aikatawa a rayuwarsu ta yau da kullum,Inda yace,da zarar an yi watsi da su to hakan takan sanyasu Shiga wasu batagari da za su lalata musu rayuwa.

Daga karshe ya yi kira ga gwamnatin jihar Kano da ta rika tunwa da irinsu Alh. Buliyaminu Takai duba da gudunmawar da suke bayarwa a cikin alumma domin dakile masu fadan daba da shaye shayen muggwan kwayoyi da kwacen wayoyin alumma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Nan gaba kadan za mu bayyana sunayen masu ɗaukar nauyin ta’addanci a Najeriya – Babban Hafsan tsaro

Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya ce...

Wasu yan daba sun ajiye Makamansu a Kano

Gwamnatin Jihar Kano Hadin gwaiwa da Rundunar Yansandan Jihar...

Masu Mukamai a gwamnatin Kano ba su da uzurin kin taimakawa yan Kwankwasiyya – Sanusi Bature

Mai magana da yawun gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin...

Magoya bayan Barr Ibrahim Isa (Matawallen Gwagwarwa) sun aikawa Gwamnan Kano Budaddiyar Wasika

Daga Isa Ahmad Getso Kira don nemawa Barr. Ibrahim Isa...