Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Date:

Zuwa ga Mai Girma
Alhaji Abba Kabir Yusuf
Gwamnan Jihar Kano
Gidan Gwamnati, Kano
Nijeriya

Mai Girma Gwamna,

Batun nadi ba bisa ka’ida ba, wajen nada Mukaddashin Shugaban Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Kano

Na rubuto wannan wasikar ne a madadin masu rajin jin kai, masana harkar shari’a, ’yan ƙungiyoyin fararen hula, da mazauna Jihar Kano masu kishin bin doka da mutunta ingancin hukumomin gwamnati.

An samu bayanai da su ka karade dandalin sada zumunta cewa Alhaji Dauda, wanda aka ce yana aiki ƙarƙashin Hon. Muhuyi Magaji Rimin Kano, ya ɗauki matakin sanar da nadin wani a matsayin Mukaddashin Shugaban Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Kano
FB IMG 1753738820016

Muna so mu bayyana  maka gaskiya bisa  girmamawa cewa iwannan nadin gaba ɗaya ba shi da tushe a doka, ya saɓa wa kundin tsarin mulki, kuma ya kauce wa dokokin Jihar Kano. Mukamin Mukaddashin Shugaban Hukumar ba wani abu ba ne da wani ma’aikaci ko shugaban sashi zai iya bayarwa—ikon nadin yana rataye ne kai tsaye a hannun Mai Girma Gwamna, kuma bisa ƙa’ida ana nadin ne ta hannun Ofishin Sakatare Gwamnatin Jiha (SSG).

Alhaji Dauda ba shi da wani matsayi na gwamnati da doka ta tanada wanda zai ba shi damar sanar da irin wannan nadin a madadin Gwamnatin Jihar Kano. Ba shi da matsayin ɗan Majalisar Zartarwa, kuma ba a naɗa shi a matsayin jami’in siyasa da ke da izinin irin wannan aiki ba. Duk wani ƙoƙari na ɗora wani shugaba a wannan muhimmiyar hukuma ba tare da bin doka ba, yana barazana ga tsarin mulki kuma ya tauye amincin da aka kafa Hukumar Yaƙi da Cin Hanci a kansa.

Mai Girma Gwamna, amincin wannan Hukuma—da kuma yadda jama’a ke kallon gwamnatinka dangane da gaskiya da shugabanci nagari—ya dogara ne da yadda ake mutunta tsarin doka. Dole ne wannan hukuma ta kasance abin koyi a fannin gaskiya da rikon amana, ba ta zama wata kafa ta biyan buƙatun wani mutum ko ƙungiya ba.

Muna kira ga Mai girma gwamnan kano

1. Soke duk wani nadin da aka yi ba bisa doka ba da ya kauce wa ingantaccen tsarin gwamnati.

2. Fitar da sanarwa daga Ofishin Sakatare Gwamnatin Jiha wadda za ta fayyace tsarin da ya dace a bi wajen naɗa mukaddashin shugaba a irin wannan hukuma.

3. Ɗaukar matakan ladabtarwa akan duk wani jami’in gwamnati ko ma’aikaci da ke ƙoƙarin kwace ikon gwamnati ko karya doka wajen gudanar da ayyuka.

Wannan ba wai al’amari ne na ƙa’ida kawai ba—muhimmin batu ne da ya shafi yadda ake sarrafa iko da kuma kare darajar hukumomi a Jihar Kano. Tarihi ya nuna cewa gwamnatinka ta tsaya tsayin daka wajen kare doka da adalci.

Muna da cikakken yakini da amincewa da jajircewarka wajen tabbatar da mulki na gaskiya da bin doka.

Na gode da kulawa da fahimta.

Da girmamawa,

Kungiyar Lauyoyin ‘Yan Asalin Kano a Ƙasa
Ta hannun: Ismail Haruna, Esq.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...

Yadda Buhari ya ƙi karɓar kyautar jirgi lokacin yana kan mulki – Garba Shehu

  Mai magana da yawun tsohon Shugaban Najeriya Muhammad Buhari,...