Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano Sheikh Ibrahim Khalil ya bukaci daliban da suka kammala makarantunsu da su rika gudanar da Murnar kammala karatunsu ta hanyoyi da suka dace .
” Ya ce ba daidai bane yadda wasu Matasa suke gudanar da bukukuwan kammala karantunsu ta hanyoyin da ba su dace da shari’a ko yan adamtaka ba, inda ya kamata yayi a Sami ɗalibi cikin nutsuwa da yin abubuwan da suka dace”.
Sheikh Ibrahim Khalil ya bayyana hakan ne lokacin da ya gabatar da jawabi a wajen bikin yayi daliban makarantar gaba da secondary ta SKYNET INSTITUTE FOR CONTINUING EDUCATION KANO KARKASHIN KWALAJIN ILIMI TA DALA .

Sheikh Ibrahim Khalil ya kara da cewa tabbas yadda abun da daliban suka yi abun a ya bane, sabanin wasu makarantun da suke gudanar da kade-kade suke shiryawa da Raye Raye.
Haka zalika shibma a nasa bangaran Tsohon babban akanta na kasar nan Alhaji Ahmad idiris (Ajiyan kasar Hausa) ya!yabawa malaman makarantar bisa yadda suke kokari wajan ganin sun koyar da daliban a fannoni daban-daban, inda ya kuma yi muzu alkawarin cigaba da gabata da tallafawa makarantar.
Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano
Alhaji Ahmad idiris ya baiwa Makarantar kyautar Naira million daya kuma ya shawarci daliban da su cigaba da neman Ilimin don inganta rayuwarsu.
Shi ma anasa jawabin shugaban makarantar Dr. Musubahu shehu tsamiya yabyi godiya ga al’ummar da suka halarci taron yaye daliban kuma yace Wannan shi ne karon farko da suka yaye daliban harkimanin Dubu biyu 2000 Amma a yau dari biyu da daya ne 201 suka iya karfar sakamakonsu .
Ya kara da cewa sun kafa wannan makaranta ne domin bunkasa harkokin ilimin matasa a wannan zamani Kuma ya hori daliban da cewa su zama masu dogaro da kawunansu domin kuwa yanzu anwuce matakin da za a gama karatu ajira sai gwamnati tabaka aikin yi.
Su ma wasu daga cikin dalibai da suka samu nasarar kammala karatun sun bayyana farin cikin da suke ciki a wannan Rana, inda suka yi godayi ga iyayen su da su ka dauki nauyin karatun su harbsuka kawo wannan mataki kumu daliban sun jadada godiyar su ga malaman su har suka kawo Wannan mataki .
Taron dai ya gudanane sani Abacha stadium dake kofar mata a jahar Kano kuma ya samu halartar manya manyan baki malamai, ,yan siyasa, yan’kasuwa da sauran al’umma ciki dawa jan jihar Kano .