Daga Rukayya Abdullahi Maida
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da ranar Juma’a 25 ga Yuli, 2025 a matsayin ranar da za a fara hutun zangon Karatu na 3 ga dukkan daliban makarantun kwana da makarantun firamare masu zaman kansu da na gaba da sakandare a jihar.
Don haka ana buƙatar iyayen da su je Makarantun ya’yansu don dauko ya’yansu da sanyin safiyar Juma’a 25 ga Yuli, 2025.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar ilimi ta jihar Balarabe Abdullahi Kiru ya fitar .
Sanarwar ta bayyana cewa daliban makarantun kwana za su koma Makaranta a ranar Lahadi 7 ga watan Satumba 2025, yayin da daliban makarantun jekaka- dawo za su koma ranar Litinin 8 ga Satumba, 2025.
Kadaura24 ta ruwaito Kwamishinan Ma’aikatar Dakta Ali Haruna Makoda ya yi kira ga Iyaye da Dalibai da su tabbatar sun bin ka’idojin da aka amince da su na komawa Makarantun ya’yansu.
Dakta Makoda ya yi gargadin cewa za a dauki matakin ladabtarwa a kan daliban da suka karya dokokin komawa Makaranta.
Ya kuma godewa Iyayen yara bisa Hadin Kai da goyon baya da suke baiwa gwamnatin jihar Kano .