Babbar kotun tarayya mai lamba shida(6) dake Babban Birnin Tarayya Abuja, ta ɗage sauraron karar da hukumar dake yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta ICPC ta shigar, bisa zargin karkatar da kuɗi a Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kano, a yayin zaɓen ƙananan hukumomin da ta gabatar na shekarar 2024 da ta gabata.
ICPC ta na tuhumar shugaban hukumar Farfesa Sani Lawan Malumfashi da ma’aikatan hukumar biyu, bisa zargin karkatar da kuɗi Naira biliyan ɗaya da da dubu ɗari biyu da ta ce an yi amfani da su ta hanyar da ta saɓa ƙa’ida.

Bayan zaman kotun na ranar Litinin 21 ga watan Yuni 2025, a ƙarƙashin jagorancin mai Shari’a J.J Malik , Kwamishinan hukumar zaɓen ta Kano Barr. Muktar Garba Ɗandago ya yi ƙarin haske kan yadda zaman kotun ya gudana.
Hakikanin halin da gwamnan Katsina yake ciki, bayan wani hatsari
“Shari’ar ita aka fara gabatarwa a kotu, kuma lauyan da ya wakilci CPC Bar. Enosa Omoghibo wanda shi ne mataimakin daraktan harkokin shari’a a hukumar, ya fara bayyana ƙorafi a kan rashin bayyanar waɗanda ake zargi a gaban kotu.”
Daga nan, sai lauyan da yake kare shugaban hukumar Zaɓen ta Kano
Bar. Mahmud Magaji SAN, ya shaidawa kotu cewar, ba a gabatar da takardar gayyata ga waɗanda ake ƙara ta hanyar da ta dace ba, hakan ya sa ba su samu damar halartar kotuba.”
Barista Ɗandago ya shaidawa manema labarai ta wayar tarho cewar, “Daga nan ne sai mai Shari’a ta J.J. Malik ta dage sauraron ƙarar zuwa 24/11/2024 domin bayar da damar gayyatar kamar yadda doka ta tanadar.” A cewar Kwamishinan hukumar Zaɓen Mai Zaman Kanta ta Jihar Kano.