Babbar Kotun Tarayya mai lamba 3 da ke Kano ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Simon Amobeda ta kori karar da jam’iyyar APC tare da Hon. Abdullahi Abbas da Hon. Aminu Aliyu Tiga suka shigar domin hana biyan kuɗaɗen kananan hukumomi a jihar Kano.
Masu ƙarar sun nemi kotun ta dakatar da biyan kuɗaɗen kananan hukumomi bisa hujjar cewa an karya umarnin kotu da ya hana gudanar da zaɓen kananan hukumomi a jihar.

A yayin zaman kotun, lauyan masu ƙara ya roƙi kotun da ta jingine sauraron shari’ar, amma lauyan gwamnatin Kano ya bukaci kotun ta kori karar gaba ɗaya tare da biyan diyya.
Hakikanin halin da gwamnan Katsina yake ciki, bayan wani hatsari
A ƙarshe, Mai Shari’a Amobeda ya yanke hukunci inda ya kori karar baki ɗaya.