Shugaban Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya iso jihar Kano domin yin ta’aziyyar hamshakin dan Kasuwar nan Alhaji Aminu Alhassan Dantata.
Jirgin da ya ɗauko Tinubu da mukarrabansa ya sauka a filin jirgin saman Aminu Kano da ke Kano da misalin karfe uku na yammacin ranar Juma’a.

Ya samu tarba daga tawagar da suka hada da jami’a gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Abba Yusuf da jiga-jigan jam’iyyar ApC na jihar Kano
Idan za a iya tunawa Alhaji Aminu Dantata ya rasu makonni uku da suka gabata lokacin da Tinubu ba ya Kasar.