ALGON ta Kano Sa’adatu Soja ta sami sabon matsayi a kungiyar ALGON ta Ƙasa

Date:

Daga: Aliyu Danbala Gwarzo.

Shugabar karamar hukumar Tudunwada kuma ALGON ta jihar Kano,Hajiya Sa’adatu Salisu Soja Maijamaa, ta samu sabon matsayin Mataimakiyar Sakataren Tsare-tsare na kungiyar Shuwagabnin kananan Hukumomi ta Ƙasa wato Deputy Organising Secretary National (ALGON).

Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman ga Shugabar ya fitar ya aikowa Kadaura24.

InShot 20250309 102512486
Talla

Hajiya Sa’adatu soja ta bayyana farin cikinta da godiyarta ga Allah bisa wannan babbar dama da aka ba ta.

Ta kuma ce tana mika godiya ta musamman ga shugabancin ALGON na ƙasa bisa amincewa da ita har ta kasance a wannan matsayi.

Da dumi-dumi: Tinubu zai zo Kano

Shugabar ta yi Addu’ar fatan gamawa lafiya tare da sauke nauyin jagoranci lafiya, da kuma tayi fatan Allah ya ba su ikon gudanar da wannan aiki cikin nasara da gaskiya.

Hajiya Sa’adatu Salisu Yusha’u soja Ta gode wa al’ummar yankin ta na Tudun wada bisa irin addu’o’i da goyon baya da suke ci gaba da nuna mata, tana mai cewa Wannan nasarar tata tamkar nasarar Alummar ce. Kasancewar sune ginshikin da take takawa

A karshe tayi kira ga Alummar yankin na Tudun wada dasu cigaba da bata hadin kai da addu’a domin samun nasar da kuma samar da cigaba a karamar Hukumar Tudun wada ta yadda Alumma zasuyi alfahari da shugabancin ta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Tinubu ya Iso Kano domin ta’aziyyar Dantata

Shugaban Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya iso jihar Kano...

Da dumi-dumi: Tinubu zai zo Kano

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai zo Kano ranar...

Tinubu ya sauya sunan jami’ar Maiduguri zuwa Sunan Muhd Buhari

Shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa...

Zargin kwace gona: Majalisar Dokokin Kano zata binciki Shugabar Karamar Hukumar Tudun Wada (ALGON)

    Majalisar dokokin jihar Kano, ta sha alwashin gudanar da...