Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya fice daga jam’iyyar PDP.
Hakan na kunshe ne cikin wata Wasika da ya sanyawa hannu da kansa kuma aikawa Shugaban jam’iyyar PDP na mazabarsa ta Jada dake jihar Adamawa.

Ya ce ya fice daga jam’iyyar ne saboda mawuyacin halin da take cikin na rashin Tabbas.
Ya godewa Shugabannin jam’iyyar bisa gudunmawar da suka ba shi tun lokacin da ya shige tun a shekarun baya.