Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Dr. Ali Makoda, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan mutuwar ɗalibai biyu a makarantar Kwana Sakandare da ke Bichi.
Ɗaliban da suka rasu, Hamza Tofawa da Umar Dungurawa, ana zargin wasu abokan karatunsu ne suka kai musu hari da wani ƙarfe da ake kira “Gwale-Gwale”.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan Wayar da Kai na Ma’aikatar Ilimi, Balarabe Kiru, ya fitar, inda aka rabawa manema labarai ciki har da jaridar The PUNCH a ranar Laraba.
A cewar sanarwar, kwamishinan, ta bakin Babban Sakataren Ma’aikatar, Bashir Muhammad, ya tabbatar wa jama’a cewa gwamnatin jihar za ta gudanar da bincike mai adalci da gaskiya tare da tabbatar da cewa kowa ya samu hakkinsa.
Kamfanin Yahuza Suya Ya aike da Sakon ta’aziyyar Rasuwar tsohon shugaban Kasa Buhari
“An bayar da rahoton cewa wannan mummunan aiki ya faru ne bayan wasu manyan ɗalibai sun yanke shawarar hukunta waɗanda suka rasu bisa zargin aikata wani laifi,” in ji shi.
Babban Sakataren, wanda ya kai ziyara makarantar, ya ja hankalin ɗalibai da su zama masu lura da kuma kaucewa ɗaukar doka a hannunsu.
“Ku guji ɗaukar doka a hannunku, ku tabbata duk wani abin da ya dame ku kun kai rahoto ga hukumomin makaranta don ɗaukar mataki da ya dace,” in ji shi.