Yadda Shugabanni da jagororin Jam’iyyar APC na Kano suka kauracewa tarbar Kashim Shattima yayi ziyarar ta’aziyya

Date:

Daga Fatima Mahmoud Diso

 

Shugabanni da jagororin jam’iyyar APC na jihar Kano sun kauracewa tarbar mataimakin shugaban Kasa Kashim Shattima, inda Jami’an gwamnatin Kano suka mamaye wajen .

Kadaura24 ta rawaito mataimakin shugaban Kasar ya zo jihar Kano ne domin yin ta’aziyyar rasuwar Marigayi Alhaji Aminu Dantata ga Iyalansa da al’ummar Kano.

Bisa al’ada an saba ganin yShugabanni da jagorori da magoya bayan jam’iyyar APC su fito su hadu da Jami’an gwamnatin Kano domin tarbar mataimakin shugaban Kasar .

InShot 20250309 102512486
Talla

Hakan tasa al’ummar jihar Kano suka fara tunanin ko dangantaka ce ta yi tsami tsakanin Shugabanni da jagororin jam’iyyar APC na Kano da Kashim Shattima ? .

Wani bincike da Jaridar Kadaura24 ta gudanar ya gano cewa kauracewa tarbar mataimakin shugaban Kasar da yan APC Kano suka yi yana da nasaba da abun da ya faru a Gombe tsakanin masoya Kashim Shattima a Arewa maso Gabas da tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa Dr. Abdullahi Umar Ganduje

Idan za a iya tunawa dai a kwanakin baya lokacin da jam’iyyar APC ta gudanar da taron ta na yankin Arewa maso Gabas an dan Sami hayaniya bayan da Ganduje lokacin Yana shugaban APC na kasa yaki ambatar sunan Kashim Shattima yayi da ya ke tabbatar da baiwa Tinubu Takarar shugaban Kasa a shekarar 2026.

Kotu ta ɗaure wani ɗan Tiktok mai wanka a tsakiyar titunan Kano

Wannan lamari shi ne ake zargin ya hana yan jam’iyyar APC na jihar Kano zuwa tarbar mataimakin shugaban Kasa Kashim Shattima .

Amma wasu kuma suna ganin hakan yana da nasaba da saukar Ganduje daga shugaban jam’iyyar APC na kasa, wanda ake zargin kamar Kashim din yana da hannu wajen saukar Gandujen.

Don tabbatar da wancan zargi ko akasin hakan Jaridar Kadaura24 ta tuntubi Mai magana da yawun jam’iyyar APC na jihar Kano Alhaji Ahmad Aruwa , Amma ba mu sami shi ba.

Mun kuma tura masa sako ta Whatsapp Amma har lokacin hada Wannan rahoto Aruwa Mai amsa sakon da muka tura masa ba.

FB IMG 1751576339311

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kotu ta ɗaure wani ɗan Tiktok mai wanka a tsakiyar titunan Kano

    Wata kotu a jihar Kano da ke arewacin Najeriya...

Damuna: Mun shirya inganta wuraren tsayarwar motocinmu – Kungiyoyin Direbobin na Kano

Kungiyar matuka motocin kurkura ta jihar Kano da Kungiyar...

Rasuwar Aminu Ɗantata babban rashi ne ba ga Nigeria kadai ba – Mustapha Bakwana

Daga Zakaria Adam Jigirya   Tsohon Mai baiwa gwamnan Kano shawarawa...

Gwamnatin Kano ta yabawa Tinubu saboda gyarawa da bude NCC DIGITAL PARK

Daga Rahama Umar Kwaru   Gwamnatin jihar Kano ta yabawa Gwamnatin...