Daga Rahama Umar kwaru
Farfesa Haruna Musa ya zama sabon shugaban jami’ar Bayero Kano (BUK), bayan nasarar zaben da ya Samu.
farfesa Haruna Musa ya samu jimillar kuri’u 853, inda ya kada sauran abokansa takarsa a zaben da aka gudanar yau talata.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwar da aka wallafa a sahihin shafin jami’ar na Facebook, inda sanarwar ta bayyana Farfesa Musa da sauran shugabannin jami’ar.
Farfesa Musa, ƙwararren malami ne da harkar gudanarwa, a halin yanzu yana aiki a matsayin Mataimakin Shugaban Jami’ar Kan harkokin gudanarwa (Academics) a BUK.
Yanzu-yanzu: Dangote ya rage farashin man fetur a Nigeria
Ga jerin yadda sakamakon zaɓen ya kasance:
1. Farfesa Haruna Musa = 853
2. Farfesa Mahmoud Umar Sani = 367
3. Farfesa Muhammad Sani Gumel = 364
4. Farfesa Adamu Idris Tanko = 161
5. Farfesa Bashir Muhammad Fagge = 18