Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Shugaban kamfanin Yahuza Suya & Catering Services Nigeria Limited, Alh. Yahuza Muhammad Idris ya bi sahun sauran ‘yan Najeriya da na sauran kasashen duniya wajen mika ta’aziyyarsa ga gwamnati da al’ummar jihar Kano bisa rasuwar Alhaji Aminu Alhassan Dantata, hamshakin attajirin kano wanda ya shahara a duniya.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Alhaji Yahuza Muhammad ya sanyawa hannu da kansa kuma ya aikowa Kadaura24 .

Sanarwar ta ce yana mika sakon ta’aziyyarsa ga gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, da Sarkin Kano na 16, Malam Muhammadu Sanusi II da ‘yan kasuwa da kuma iyalan marigayin.
Alh. Yahuza Muhd Idris ya bayyana rasuwar Alhaji Dantata a matsayin babban rashi ga ‘yan kasuwar duniya, musamman na yankin Sahara.
Shugaban Yahuza Suya & Catering Services Nigeria Limited ya kara da cewa al’umma da dama sun amfana da arzikinsa ta hanyar ba su aiyukan yi a kamfanoninsa da kuma aiyukan jin Kai da ya rika gabatarwa a cikin al’umma.
Yanzu-yanzu: Dangote ya rage farashin man fetur a Nigeria
Ya kara da cewa, ba shakka za a iya rika tunawa da marigayi Dantata a matsayin daya daga cikin wadanda suka ba da gudunmawa sosai wajen ci gaban tattalin arzikin Nijeriya, musamman Kano, cibiyar harkokin Kasuwanci Arewacin Nijeriya.
Ya yi addu’ar Allah ya gafarta masa kurakuransa, ya saka masa da kyawawan ayyukansa da aljannah firdausi sannan ya bukaci ‘yan uwa da abokan arzikinsa da su yi hakuri da Wannan Babban rashin.