Labari Mai Daɗi: Asibitin Kwararru Na Best Choice Ya Rage Kaso 50 Na kuɗaɗen Ayyukansu Tare Da Buɗe Fayal Kyauta

Date:

 

 

Asibitin Kwararru Na Best Choice Ya Rage Kaso 50 na kuɗaɗen ayyukansu na yau da kullum, wanda suka haɗa da kudin ganin likita kudin Gado da sauran ayyukan su, shi kuma bude Fayal ya zama kyauta ne yanzu haka.

Hakan na kunshe ne Cikin wata tattaunawa da shugaban asibitin Alh Auwal Muhd Lawal yayi da Jaridar Alfijir Labarai a yau Talata.

InShot 20250309 102512486
Talla

Lawal yace bayan korafe-korafe da kiraye-kirayen da jama a suke ta yiwa asibitin hukumar gudanarwar sun yi kwakkwaran bincike har suka gano yadda wasu suke kasa zama har lokacin da ya dace likita ya sallamesu yayi suke tafiya, sannan wasu kuma tun daga bude fayil suke kasawa duk da yadda suke kaunar zuwa asibitin, wannan dalilin ne yasa suka ɗauki wannan matakin domin farantawa al’umma duk da irin kuɗaɗen da suke kashewa ga tsadar komai ga kuma yadda ake bawa asibitin cikakkiyar kulawa.

A baya muna buɗe fayil na mutum daya akan dubu 20, shi kuma na iyali dubu 40 yanzu haka ya koma kyauta.

Fadan daba: ku fito ku Kare Kan ku da iyayenku – Gwamnatin Kano ga matasa

Shi kuma ganin likita dubu 10 ne, amma yanzu ya koma dubu 5. Kudin gado dubu 70 ne, amma yanzu mun mai dashi dubu 35 babban dakin, akwai na dubu 50, ya koma dubu 25,  dakin dubu 25, ya koma dubu 12,500, sai ɓangaren masu awo shine daga dubu 150,000 ya koma dubu 80, haihuwa itama daga dubu 150,000 ta koma dubu 80, sai CS daga dubu dari 6, ya dawo dubu dari 3, haka sauran gwaje-gwajen ma duk suma haka zasu koma domin a kara kyautatawa al’umma, Allah ya kare mu da lafiya baki daya ameen.

A karshe a madadina da iyalaina da maaikatana Muna mika ta’aziyyarmu ga iyalan Marigayi Alh Aminu Dantata da gwamnatin Kano da al’ummar Kano da Afrika baki ɗaya.

IMG 20250415 WA0003
Talla

Asibitin Kwararru Na Best Choice yana nan a mazauninsa na dindindin dake Plot 782/783 tal’udu kusa da makarantar Sheikh Bashir Eli Rayya kuma muna aikinmu ba dare ba rana tare da manyan likitoci.

Za a iya tuntubar mu ta yanar gizo bestchoiceclinic@gmail.com
bestchoiceclinic@yahoo.com
Ko facebook Best Choice Specialist Hospital.

Ko kira da whatsapp akan +2347034951671
+234912 345 3534
+2342082443318

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: An zabi sabon shugaban jami’ar Bayero BUK

Daga Rahama Umar kwaru   Farfesa Haruna Musa ya zama sabon...

An sake sauya lokacin jana’izzar Aminu Ɗantata – Gwamnatin Nigeria

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta ce Hukumomi a Kasar Saudiyyar...

Fadan daba: ku fito ku Kare Kan ku da iyayenku – Gwamnatin Kano ga matasa

Ku tashi ku Kare kanku da iyayen Gwamnatin jihar kano...

Rasuwar Aminu Ɗantata babban rashi ne ga Duniya baki daya – Shugaban kamfanin Yahuza Suya

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Shugaban kamfanin Yahuza Suya & Catering...