Matatar mai ta dangote ta rage farashin man fetur daga Naira 880 zuwa N840 kowace lita.
Kakakin Rukunin kamfanoni Dangote, Anthony Chiejina, ya tabbatar wa da jaridar PUNCH cewa an rage farashin a daren ranar Litinin.

Ya ce sabon farashin ya fara aiki ne a ranar 30 ga watan Yuni.
“An rage farashin man daga N880 zuwa N840 kowace lita daga 30 ga watan Yuni,” Chiejina
Idan za a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito matatar man Dangote ta kara farashin man fetur zuwa naira 880 a daidai lokacin da rikici ya barke tsakanin Isra’ila da Iran na tsawon kwanaki 12, lamarin da ya sa farashin danyen mai ya Karye akan dala 80 kan kowacce ganga.
Da dumi-dumi: An Sanya dokar Hana fita a Kaduna
A baya dai jaridar PUNCH ta ruwaito cewa ‘yan kasuwar sun yi hasashen za a iya kara farashin daga ranar Litinin.
Abokan huldar matatar Dangote irinsu MRS, Heyden da AP ana sa ran za su rage farashin na su nan ba da jimawa ba.