Ra’ayin Bashir A Bashir
A yayin da ake kara bukatar shugabanni masu kishin al’umma, wadanda ke mayar da alkawari aiki, Honarabul Hassan Shehu Hussain, dan majalisar wakilai na tarayya mai wakiltar mazabar Nassarawa, ya ci gaba da zama abin koyi na wakilci nagari.
Kafa Cibiyar Maganin Cutar Zuciya a AKTH
Daya daga cikin manyan nasarorin da Hon. Hussain ya cimma a wannan wa’adin nasa shi ne yadda ya jagoranci wucewar kudurin kafa Cibiyar Maganin Cutar Zuciya (Heart Washing Center) a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH).

Wannan ci gaba na tarihi, ya sanya Kano cikin jerin jihohin da ke da cibiyar kulawa da marasa lafiya masu fama da cututtukan zuciya a Najeriya. Wannan nasara ta jaddada irin damuwar da Hon. Hussain ke yi game da lafiyar al’umma.
A kokarinsa na rage yawan matasa da ke zaman kashe wando, Hon. Hassan Hussain ya taka muhimmiyar rawa wajen samar da guraben aiki ga matasan mazabarsa a Hukumar Kwastam ta Najeriya (Nigeria Customs Service). Wannan mataki ya sauya rayuwar matasa da dama, tare da rage radadin rashin aikin yi.
Har wa yau, ya gabatar da kuduri a majalisar wakilai domin kafa kwamitin farfado da masana’antun da suka durkushe a yankunan Bompai da Chalawa. Wannan kuduri yana daga cikin matakan da za su taimaka wajen farfado da masana’antu da kuma samar da karin ayyukan yi ga matasa.
Ginin Tituna Da Fitilun Zamani
A bangaren ci gaban ababen more rayuwa, Hon. Hussain ya aiwatar da gine-ginen tituna a sassa daban-daban na mazabar Nassarawa, tare da sanya fitilu na zamani a kan titunan. Wannan ya kara bunkasa harkokin kasuwanci da zirga-zirgar dare, da kuma tabbatar da tsaro a yankin.
Gina Ajujuwa: Taimakawa Ilimi
A bangaren ilimi, Hon. Hassan Hussain ya gudanar da gina sabbin ajujuwa a makarantu da dama da ke fama da cunkoso. Wannan ya taimaka wajen rage yawan dalibai a aji daya, da kuma bunkasa yanayin koyarwa da koyo.
Sabbin Ayyuka a Dakata Ward
Baya ga abubuwan da ya riga ya aiwatar, Hon. Hussain yana shirin fara aikin gina sabuwar asibiti da hanyar mota a Dakata Ward. Wannan wani bangare ne na kokarinsa na kara inganta rayuwar al’umma ta fuskar kiwon lafiya da zirga-zirga.

Wakili Mai Aiki, Ba Magana Kawai Ba
Ba tare da nuna shakku ba, Hon. Hassan Shehu Hussain ya tabbatar da kansa a matsayin wakili mai aiki, wanda ke mayar da wakilcinsa aikin yi, ba zantuka kawai ba.
Jama’ar Nassarawa na ci gaba da jin dadin wakilcinsa, tare da fatan ganin karin ayyuka masu amfani a nan gaba