Kwamandan Jami’an sintiri na karamar hukumar Nasarawa a jihar Kano Muhammad Haruna Yahya Black ya ja hankalin al’umma da su ci gaba da baiwa jami’an yan sintiri hadin kai don inganta tsaro a fadin jihar.
Kwamanda Muhammad Haruna Bulak ya bayyana hakan ne yayin da ya kai wata ziyara unguwar gani da ido da ya kai unguwar Haye, inda ake zargin wani guri a unguwar na neman zama matatarar bata gari a unguwar.

Ya ce sun shirya tsaf domin ganin su kakabe duk wasu bata garin dake neman mamaye yankin a matsayin mafakarsu.
Muhammadu Haruna yahaya Black ya ce nan ba da jimawa ba za su kafa ofisdinsu a yanki domin kawo karshe bata garin da suke neman mamaye yankin.
Yanzu-Yanzu: An ɗage jana’izar Aminu Ɗantata saboda wasu dalilai
Ya kara da cewa baza su gajiya ba wajan ganin sun kawo karshen fadan daba da kuma kwacen waya a jihar Kano da ya ke neman ga garak kundila a jahar Kano
Kwamandan Kuma ya yi kira ga masu ruwa da tsaki dama uwa uba gwamnati du su rika tallafa musu da kayayakin aiki domin gudanar da aikinsu
Daga karshe Muhammadu Haruna yahaya Bulak ya ja hankalin jami’an su da su ci gaba da riko da gaskiya da amana wajan gudanar da aikinsu.