Kungiyar ’Yan Jaridun Kano Arewa ta Aike da Sakon Ta’aziyyar Rasuwar Alhaji Aminu Dantata

Date:

 

Kungiyar ’Yan Jarida ta Kano Arewa ta bayyana alhinin ta sakamakon rasuwar fitaccen attajiri kuma jigo a harkar kasuwanci a Najeriya, Alhaji Aminu Alhassan Dantata, wanda ya rasu yana da shekaru 94.

Rasuwar Alhaji Aminu Dantata babban rashi ne, ba ga iyalansa da al’ummarsa kawai ba, har ma ga Jihar Kano, Arewacin Najeriya da kasar baki ɗaya. Gudummawar da ya bayar a fannin kasuwanci, aikin alheri, ilimi da ci gaban addini sun bar tarihi da ba za a manta da su ba har tsawon zamani.

InShot 20250309 102512486
Talla

Alhaji Aminu Dantata mutum ne da aka girmama, jagora kuma uba ga ɗaya daga cikin manyan gidajen kasuwanci da suka fi kowa kima a Najeriya da nahiyar Afirka. Rayuwarsa ta cika da gaskiya, tawali’u da hidima ga al’umma.

Ku na da rawar takawa wajen inganta Lafiyar al’ummar Kano – Waiya ga jami’an yada labarai

A madadin mambobin kungiyar gaba ɗaya, ƙarƙashin jagorancin Comrade Shuaibu Sani Bagwai, muna jajanta wa dangin mamacin da dukkan al’ummar Najeriya bisa wannan babban rashi. Muna roƙon Allah Madaukakin Sarki Ya gafarta masa, Ya jikan sa da rahama, Ya ba shi mafaka a Aljannatul Firdaus, sannan Ya bai wa iyalansa da kasa baki ɗaya haƙuri da juriyar rashin sa.

Ko da ya bar duniya, tarihi da kyakkyawar gadon da ya bari za su ci gaba da rayuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: An Sanya dokar Hana fita a Kaduna

Gwamnatin Kaduna ta sanya dokar taƙaita zirga-zirga ta tsawon...

Yanzu-Yanzu: An ɗage jana’izar Aminu Ɗantata saboda wasu dalilai

Gwamnatin Najeriya ta sanar da ɗage jana'izar fitaccen ɗankasuwar...

Kungiyar Farfado da martabar Arewa ta Mika sakon ta’aziyyar Rasuwar Aminu Dantata

Daga Sadiya Ahmad   Kungiyar Farfado da martabar Arewa ta Mika...

Ku na da rawar takawa wajen inganta Lafiyar al’ummar Kano – Waiya ga jami’an yada labarai

Daga Abubakar Sayeed Kwamishinan Ma'aikatar yada labarai da harkokin cikin...