Kungiyar Farfado da martabar Arewa ta Mika sakon ta’aziyyar Rasuwar Aminu Dantata

Date:

Daga Sadiya Ahmad

 

Kungiyar Farfado da martabar Arewa ta Mika Sakonta na ta’aziyya ga gwamnatin jihar Kano da iyalai marigayi Alhaji Aminu Dantata wanda ya rasu a ranar asabar data gabata.

A wata sanarwa da shugaban kwamitin amintattu na kungiyar Alhaji Gidado Muktar da daraktan yada labarai Mahmoud Adnan Audi suka fitar, kungiyar ta bayyana rasuwar Aminu Dantata a matsayin babban rashi ba ga Kano kadai ba, har ma da yankin Arewa da ma kasa baki daya.

InShot 20250309 102512486
Talla

A cikin sanarwar, NRO ta ce rasuwar Dantata ta haifar da gibi mai yawa a harkar kasuwanci a Najeriya, inda ta yaba da irin gudunmawar da ya bayar wajen bunkasa masana’antu da bunkasar tattalin arzikin Nigeria da Africa baki daya

‘Aminu Dantata ya taka rawar gani wajen habaka kasuwanci da masana’antu a Kano kuma a shekaru da dama, kuma ya rasu ne a lokacin da ake bukatar hikimarsa da gogewarsa wajen ci gaban tattalin arzikin Najeriya.

Ku na da rawar takawa wajen inganta Lafiyar al’ummar Kano – Waiya ga jami’an yada labarai

Kungiyar NRO ta yiwa iyalansa da ‘yan kasuwa da gwamnatin jihar Kano ta’aziyyar Dantata wanda ya dade ya na sadaukar da rayuwarsa wajen mai taimakon al’umma.

Sannan kungiyar ta yi masa addu’ar Allah ya ba shi matsayi mafi girma a cikin Jannatul Firdaus, ya kuma baiwa iyalansa hakurin jure rashin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Muna bukatar kayan aiki domin magance matsalar tsaro a karamar hukumar Nasarawa – Muhd Haruna Black

Kwamandan Jami'an sintiri na karamar hukumar Nasarawa a jihar...

Da dumi-dumi: An Sanya dokar Hana fita a Kaduna

Gwamnatin Kaduna ta sanya dokar taƙaita zirga-zirga ta tsawon...

Yanzu-Yanzu: An ɗage jana’izar Aminu Ɗantata saboda wasu dalilai

Gwamnatin Najeriya ta sanar da ɗage jana'izar fitaccen ɗankasuwar...

Kungiyar ’Yan Jaridun Kano Arewa ta Aike da Sakon Ta’aziyyar Rasuwar Alhaji Aminu Dantata

  Kungiyar ’Yan Jarida ta Kano Arewa ta bayyana alhinin...