Tawagar da gwamnatin Najeriya ta tura zuwa Madina na ƙasar Saudiyya domin halartar jana’izar Alhaji Aminu Ɗantata tuni ta isa ƙasar.
Attajirin ɗan kasuwar wanda ya rasu a ƙarshen mako ya bar wasiyyar cewa yana so a birne shi a garin Manzan Allah, burin da hukumomin Saudiyya suka amince da shi.

A ɓangaren gwamnatin tarayya tawagar na ƙarƙashin jagorancin ministan tsaro kuma tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar.
Rashin Alhaji Aminu Dantata Babban Rashi ne ga harkokin kasuwanci a Duniya – Salbas
Sauran mambobin tawagar sun haɗa da ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, Lateef Fagbemi (SAN) da ministan yaɗa labarai, Alhaji Mohammed Idris, da ƙaramin ministan gidaje da raya birane, Hon. Yusuf Abdullahi Ata da dai sauran su.
Akwai kuma manyan malamai a cikin tawagar da suka haɗa da sheikh Aminu Daurawa da Dr Bashir Aliyu Umar da kuma Khalifa Abdullahi Muhammad.