Rasuwar Aminu Dantata: Duniyar Kasuwanci ta yi Babban Rashi – Shugaban Kamfanonin Gerawa

Date:

Shugaban rukunonin Gerawa group of Companies Dr. Ibrahim Muhammad Gerawa ya bayyana rasuwar marigayi Alhaji Aminu Dantata a matsayin Babban rashi ga masu harkokin kasuwanci a Duniya baki daya.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mataimaki na musamman Kan harkokin yada labarai na kamfanonin Gerawa Com. Babangida Mamuda Biyamusu wand ya aikowa Kadaura24 a Kano.

InShot 20250309 102512486
Talla

Kamfanin ya bayyana rasuwar Alhaji Dantata a matsayin babban rashi da ya ba za jihar Kano Kadai akaiwa ba, har ma Nigeria Africa da Duniyar harkokin kasuwanci baki daya.

Sanarwar ta yi kira ga attajiran kasarnan da su yi koyi da halin attajirin na jinkan al’umma da taimakawa masu karamin karfi.

A Gaggauce: Fadar shugaban Kasa ta musanta murabus din Sakataren gwamnatin tarayya

“Ni Shugaban kamfanin, Alhaji Dr. Ibrahim Gerawa Ina mika ta’aziyyarta ga gwamnatin jihar Kano, da yan uwan da abokai da iyalan Alhaji Aminu Dantata bisa Wannan gagarumin rashini”. Inji Gerawa

Ya ce za a rika tunawa da Alhaji Aminu Dantata da hangen nesansa, jagoranci, da karamcinsa, tare da bayar da gudunmawarsa ga harkokin kasuwanci, ayyukan jin kai, da ci gaban al’umma, tabbas ya bar tarihi da ba a taba mantawa da shi ba.

GMD Alhaji Ibrahim Muhammad Gerawa ya kuma yi addu’ar Allah ya ji kan Alhaji Dantata ya sa ya huta, kuma ya ba iyalansa hakurin jure wannan babban rashin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Wasu kungiyoyin APC a Kano sun fara kiraye-kirayen Abdullahi Abbas ya sauka daga shugaban jam’iyyar

Daga Hafsat Abdullahi Muhammad Kungiyoyin jam'iyyar APC da suka hadar...

Bayan Amincewar Kasar Saudia , an Sanya Ranar Binne Aminu Dantata a Madina

Babban sakataren marigayi Alhaji Aminu Dantata, Mustapha Abdullahi Junaid...

Rashin Alhaji Aminu Dantata Babban Rashi ne ga harkokin kasuwanci a Duniya – Salbas

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Babban kamfani a masana'antar mai a...

NNPPn Kano ta bayyana matsayar Kwankwaso kan batun yi wa Tinubu mataimaki a 2027

Shugabanin bangarori biyu na jam’iyyar NNPP a jihar Kano,...