Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Babban kamfani a masana’antar mai a Nigeria Salbas Oil and Gas ya bayyana rasuwar marigayi Alhaji Aminu Dantata a matsayin Babban rashi ga masu harkokin kasuwanci a Nahiryar Africa baki daya.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da makusancin Shugaban kamfanin Aliyu Harazimi Rano ya aikowa Kadaura24 a kano.

Kamfanin ya bayyana rasuwar Alhaji Dantata a matsayin babban rashi da ya zarce jihar Kano da Najeriya, wanda ya shafi harkokin kasuwanci a duniya.
“Shugaban kamfanin, Alhaji Sale Baba Rano, na mika ta’aziyyarsa ga gwamnatin jihar Kano, da yan uwan da abokai da iyalan Alhaji Aminu Dantata yana kuma yi masa fatan samun rahamar Allah madaukakin Sarki”.
NNPPn Kano ta bayyana matsayar Kwankwaso kan batun yi wa Tinubu mataimaki a 2027
Ya ce Babban abin da za a rika tunawa da Alhaji Aminu Dantata saboda hangen nesansa, jagoranci, da karamcinsa, tare da bayar da gudunmawarsa ga harkokin kasuwanci, ayyukan jin kai, da ci gaban al’umma, tabbas ya bar tarihi da ba a taba mantawa da shi ba.
Ya kuma yi addu’ar Allah ya ji kan Alhaji Dantata ya sa ya huta, kuma ya ba iyalansa hakurin jure wannan babban rashin.