Daga Hafsat Abdullahi Muhammad
Kungiyoyin jam’iyyar APC da suka hadar da Kungiyar kadan garen bakin tuku da ta yan takwas sun yi kira ga Shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano Abdullahi Abbas da ya sauka daga kan kujerar shugabancin jam’iyyar saboda rigingimun da ya haifar a jam’iyyar.
Shugaban kungiyar yan takwas na jam’iyyar APC Nura Na’annabi da sakataren kungiyar APC Kadangaren Bakin Tulu Kwamared Abubakar Abdullahi Dangarinnan su ne suka bukaci hakan yayin wani taron manema labarai .

“A Madadin Kungiyar APC kadangaren Bakin Tulu ta Jihar Kano, Muna yabawa Dr. Abdullahi umar Ganduje bisa Amsa kiraye kirayenmu da muka dade
munayi na cewa ya sauka daga wannan kujera ta Shugaban Jam’iyar APC na Kasa, duba da irin rigingimu da zamansa a wannan kujerar ya haifar, Muna yaba Masa bisa irin kokarin da yayi na ganin an samu shigowar wasu daga ikin Gwamnoni da Sanato da Yan’Majalisar Tarayya dana Jihohi zuwa wannan Jam’iyar, Hakika abin a yaba masa ne Muna Masa fatan Alheri a duk inda ya tsinci Kansa nan Gaba. ”
Bayan Amincewar Kasar Saudia , an Sanya Ranar Binne Aminu Dantata a Madina
Muna so kuma muyi Amfani da wannan dama domin taya sabon Shugaban riko na Jam iyar APC His Excellency Bukar Dalori murnar kama aiki muna Addu’a Allah ya dafa masa. Sannan muna so muyi Kira gare shi cewa yayi Gaggawar rushe Shugabancin Jam’iyara Matakin Jihohi Musamman na nan Jihar Kano, yin haka zai dawowa da Jam’iyar APC ta Jihar Kano Kwarjinin data rasa tun bayan kasancewar Hon. Abdullahi Abbas a Matsayin Shugaban ta na Jihar Kano”.
Com. Dangarinnan ya ce “Idan kuma Allah yasa yaji kiraye kirayen da muke na cewa ya gaggauta sauka to Alhamdulillah. Muna kuma Kira gashi sabon Shugaban Jam’iyar APC na Kasa cewa Lokaci yayi da zaiyi kokar Wajen dinke kowace irin baraka da Shugabancin su Ganduje da Abdullahi Abbas suka haifar mana na raba raben kawunan Yan’ Jam’iyyar Musamman a nan Jihar Kano.

Ya kuma ce za’a dade ana tunawa da Jagoranci Bolari idan har ya yi kokarin dawo da Muhimman Mutane masu Daraja iin su Jagora Dr Rabiu Musa Kwankwaso zuwa wannan Jam’iya tamu Mai Albarka. Domin kowa yasan irin Gudummawar dasu Dr. Rabiu Musa Kwankwaso suka bayar Wajen Tabbatar da Nasarar Jam’iyyar tun daga kafata a Shekarar 2014 har zuwa Lokacin dasu Ganduje suka hada kai da wasu domin ganin yabar Jam’iyyar.
Daga karshe muna sake Kira ga Shugaban Jam’iyar APC na Kano cewa
Lokaci yayi dazai sauka domin bawa masu Kishin Cigaban Jam’iyar APC dama domin Tabbatar da Nasarar Jam’iyar a zaben Shekara ta 2027 In Sha Allah.