Daga Rukayya Abdullahi Maida
Shugaban Hukumar tace fina-finai da Dab’i ta Jahar Kano Alh. Abba ya jaddada aniyarsa ta kawo karshen aiyukan rashin da’a da ke yawaita a kafafen sada zumunta na zamani a Jahar Kano.
El-mustapha ya bayyana hakan ne a yau, bayan da Hukumar ta samun nasarar kama ABUBAKAR KILINA sanannan mai amfani da manhajar TikTok a wani salo na shigar mata da wasu halayya da ake zargi ta nuna rashin tarbiya tare da kalamai marasa ma’ana inda la’akari da yin hakan laifi ne, Hukumar ta yanke shawarar kaishi gaban kotu domin girbar abin da ya shuka.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a hukumar Abdullahi Sani Sulaiman ya aikowa Kadaura24.
Tun da farko bayan mai gabatar da Kara Bar. Garzali Maigari Bichi ya karantowa wanda ake zargi tuhume-tuhumensa wato ABUBAKAR KILINA nan take ya amsa dukkannin laifukan shi sai dai mai shari’ar da ke kotun ta noman’s-land Hajiya Halima wali ta dage sauraron karar daga 4/6/2025 zuwa 17/6/2025 tare da bada umarnin a ajiyesu a gidan gyaran hali har ranar da za’a dawo domin yanke hukunci.
Rabon Jakai: Faizu Alfindiki ya aikawa Sanusi Bature budaddiyar wasika
Idan ba’a mantaba a watannin da suka gabata Hukumar tace fina-finai da Dab’i ta Jahar Kano ta aike da irin wannan matasa gaban kotu domin ladaftar dasu inda kotun bayan samunsu da laifi kotun ta yanke musu hukuncin daurin shekara daya ko zabin biyan tara na kudi nera dubu Dari daya (100,000) tare da wanda zasu karbesu da sharadin irin haka bazai kara faruwa dasu ba.
Wannan dai wani yunkuri ne da Hukumar tace fina-finai ta Jahar Kano ke yi tsawon lokaci domin kawo gyara tare da dakile irin rashin tarbiyar da wasu matasa ke nunawa a kafafen sada zumunta a Jahar Kano wanda yin hakan yaci karo da tsarin al’ada tare da koyarwar addinin musulunci.