Iftila’i: Wakilan Kano 21 a gasar wasanni ta kasa sun rasu, yayin wani haɗari a hanyar da dawowa gida

Date:

Kimanin Mutane 21 ne daga cikin tawagar da ta wakilci jihar Kano a gasar wasanni ta ƙasa da aka kammala kwanan nan, wanda aka gudanar a jihar Ogun su ka mutu a hatsarin mota.

DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa kimanin motocin bas guda 30 ne dauke da tawagar yan wasa ta Kano su ka taso daga Ogun a ranar Alhamis da daddare inda suka isa Kano lafiya.

IMG 20250415 WA0003
Talla

Sai dai motar karshe ta yi hatsari, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 21 kawo yanzu, yayin da sama da 10 suka samu munanan raunuka.

Al’ummar Kano ku baiwa AA Zaura hadin Kai domin ya kawo karshen fadan Daba – Baba Yawale

Wani jami’in tafiya mai suna Ado Salisu ya shaida wa wakilinmu cewa lamarin ya faru ne a gadar Dakatsalle da ke karamar hukumar Garun Malam da misalin karfe 8 na safiyar yau Asabar, inda motar bas din ta daki rami ta kuma wuntsila.

Salisu ya ce 19 daga cikin ƴan wasan da suka hada da jami’ai sun mutu nan take yayin da wasu biyu kuma suka rasu a babban asibitin karamar hukumar Kura.

InShot 20250309 102403344

A cewar Salisu, daga cikin wadanda suka rasu akwai kakakin hukumar wasanni ta jihar Kano, Ibrahim Galadima.

Ya ce fasinjojin da suka jikkata na samun kulawa a asibiti yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen daukar gawarwakin wadanda suka mutu ga iyalansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Likitocin Jinya da Ungozoma sun janye yajin aiki – Ministan lafiya

Ƙungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Ƙasa (NANNM) ta...

Sarkin Hausawan Arewa, Amb. Balarabe Tatari, Ya Aike da Sakon Ta’aziyyar Buhari da Dantata

Sarkin Hausawan Arewa kuma Ambasadan Zaman Lafiya, Alhaji Balarabe...

INEC ta sanya ranar fara rijistar masu zabe a Nigeria

Hukumar zaɓen Najeriya ta ce nan gaba cikin wannan...