Karyewar gada ya jefa dubban al’umma cikin mawuyacin hali a Rano, Sun nemi Agajin Gwamnan Kano

Date:

Daga Maryam Muhammad Ibrahim

Al’ummar garuruwan Kazaurawa/Unguwar Ganji da ke karamar hukumar Rano a Jihar Kano, na cikin fargaba da tashin hankali saboda lalacewar hanyarsun da karyewar gada ga kuma yadda damina ke neman kankama.

Hanya ita ce daya tilo da ta hada yankin da al’ummomin da ke kewaye ta fada cikin mummunan yanayi, lamarin da ya haifar da fargabar da tashin hankali da kuma karuwar wahala ga al’ummar yankin.

IMG 20250415 WA0003
Talla

Da yake jawabi a madadin al’ummar yankin, kakakin karamar hukumar Rano, Hon.Ahmed Abdullahi Jibrin, ya bayyana takaici da fargabar mawuyacin halin da mazauna yankin za su sake shiga sakamakon rashin hanya ga kuma damuna.

Ya ce:”Halin da hanyar ta ke a halin yanzu ya sanya al’ummar mu cikin mawuyacin hali musamman a lokacin da damina ke kara gabatowa, hanyar ta lalace gadar kuma ta karye wacce da ita al’ummar yankin suke amfani wajen zuwa muhimman wurare kamar asibitoci, kasuwanni, da makarantu, manoman mu ma ba sa iya fitar da amfanin gonakin da suka noma, wanda hakan ke shafar rayuwarsu.”

Ban ce filin makarantar Bechi nawa ba ne, Kuma zan taimaka wajen gini Makarantar -Alh. Sagir Jaen

Ahmad Abdullahi ya kuma yi kira ga gwamnatocin Jihi da tarayya da su kai musu dauki cikin gaggawa domin sake gina hanyar, yana mai jaddada cewa matukar ba a gyara hanyarba al’ummar yankin za su cigaba da kasancewa cikin fargaba da tashin hankali wanda hakan zai shafi walwalarsu da tattalin arzikimsu saboda muhimmancin hanyar.

Shima da yake jawabi, wani dattijo a yankin Alhaji Wada Kazaurawa, ya jaddada cewa hanyar ta hada akalla garuruwa bakwai — daga garin Rurum zuwa Bakin Fa, Kazaurawa Ghana, Gunduma,Gidan GANJI,Bul,Saya saya — a karshe ya hade da kananan hukumomin Kibiya da Tudun Wada.

Ya kuma bayyana cewa, an yi watsi da aikin gina wasu muhimman gadoji guda biyu da ke kan titin kimanin shekaru 14 da suka gabata.

InShot 20250309 102403344

“Abin takaici, mata masu juna biyu da yawa sun rasa rayukansu sakamakon rashin kai su asibiti l,” in ji shi.

A wata sanarwa da jami’in yada labarai na shiyyar Rano Rabi’u Khalil Kura ya aikowa Kadaura24 ya ce Mazauna yankin sun yin kira ga hukumomin da abin ya shafa da su gaggauta yi musu aikin hanyar tun kafin damina ta fadi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Gwamnatin Kano ta Haramta “Kauyawa Day”

Daga Nasiba Rabi'u Yusuf   Hukumar tace fina-finai da dab'i ta...

Inganta ilimi: Shugaban Karamar hukumar Ungoggo ya kaddamar da rabon kayan koyo da koyarwar

Daga Shehu Usaini Getso Shugaban karamar hukumar Ungoggo Alhaji Tijjani...

Rashin tsaro: Tinubu na ganawar sirri da shugabannin hukumomin tsaro na ƙasa

A halin yanzu shugaba Bola Ahmed Tinubu ya na...

Ban ce filin makarantar Bechi nawa ba ne, Kuma zan taimaka wajen gini Makarantar – Alh. Sagir Jaen

Daga Maryam Muhammad Ibrahim Biyo bayan koken da al'ummar garin...