Tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya yi watsi da wasu rahotanni da a ke yadawa a kafafen sada zumunta da ke bayyana matsayarsa kan siyasar Nijeriya.
Cikin wata sanarwa da ya fitar a hukumance, Kwankwaso ya ce wadancan rahotanni ba gaskiya ba ne.

Ya ce a yanzu ya tsame hannu daga cewa wani abu dangane da tataburzar siyasa a Nijeriya, domin a cewarsa lokacin bayyana matsayarsa bai yi ba tukuna.
Da dumi-dumi: Gwamnatin Kano ta Haramta “Kauyawa Day
Ya yi kira ga al’umma da su yi fatali da wadancan labaran karya.
Idan za a iya tunawa anyi ta yada cewa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce ba shi ba zai koma jam’iyyar APC dake mulkin Nigeria ba.