Daga Isa Ahmad Getso
Gwamnatin Jihar Kano za ta duba yiwuwar hada kai da Jami’ar Bayero, Kano, domin baiwa masu yada aiyukan gwamnatin Abba Kabir Yusuf a kafafen sada zumunta damar yin difloma don inganta aikin na su.
Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya bayyana hakan a yayin bikin rufe taron karawa juna sani na yini biyu da Ma’aikatar Yada Labarai ta shiryawa yan soshiyar midiya .

Kwamared Waiya ya bayyana cewa, idan matasan suka sami damar yin kwas din zai kara musu damar yin amfani da kafafen sada zumunta yadda ya kamata wajen yada bayanai da manufofi da aiyukan gwamnatin Kano.
Kwamishinan ya kara da cewa gwamnatin jihar tana daukar yan soshiyar midiya a matsayin jakadunta, don haka ya bukace su da su kasance masu yada aiyukan gwamnatin Kano ba wai cin mutuncin mutane ba.
Gwamna Kano zai Baiwa Malaman Makarantu Bashin Ababen Hawa Motoci Naira Miliyan 200 A Kano
Waiya ya ce akwai bukatar yan soshiyar midiyan su rika gudanar da bincike don ribatar damammakin kasuwanci da ake da su a shafukan sada zumunta don su zamo masu dogaro da kawunansu.
A jawabinsa na godiya, Shugaban kungiyar masu yada aiyukan gwamnatin Kano a Twitter ya yabawa ma’aikatar yada labarai da harkokin cikin gida bisa shirya taron, wanda ya basu damar samun karin kwarewa da ilimi domin inganta yada ayyukan gwamnati.

A wata sanarwa da daraktan aiyuka na musamman ga ma’aikatar yaɗa labarai Sani Abba Yola ya sanyawa hannu kuma ya aikowa Kadaura24, ya ce a yayin taron malamai da dama sun gabatar da kasidu da dama.
A karshen taron, mahalarta taron sun bayar da lambar yabo ga Kwamishinan bisa la’akari da yadda ya himmatu wajen ganin an yada aiyukan gwamnatin Abba Kabir Yusuf bisa kwarewa da ilimi.