Allah ya yi wa dattijo, kuma Sakataren kungiyar Northern Reform Organisation (NRO) Injiniya Abdulkadir Yusuf Gude rasuwa .
Injiniya Abdulkadir Yusuf Gude ya rasu ne a ranar Juma’a yana da shekaru 65 bayan ya sha fama da rashin lafiya.

Injiniya Gude, wanda aka sani da jajircewa wajen ganin an kawo sauyi a yankin arewacin Najeriya da ma kasa baki daya, ya na daya daga Shugabannin kungiyar NRO na farko, wadda aka kafa ta domin tunkarar kalubalen da yankin arewa ke fuskanta.
Gwamnatin da ta ke korar Ma’aikata ba ta Cancanci Wa’adi na biyu ba – Faizu Alfindiki
Ya yi aiki a hukumar WRECA na tsawon shekaru, sannan kuma ya yi aiki a kamfanin Aluminum Smelter da sauransu.
Wani makusancinsa Mahmoud Adnan Audi ya tabbatar da rasuwarsa, inda ya ce za a yi jana’izar marigayin da misalin karfe 2:30 na rana bayan sallar Juma’a a tsohuwar Jami’ar Bayero Kano.
Allah ya gafarta masa kurakuransa, ya saka masa Jannatul Firdaus.