Sanarwa ta Musamman daga kungiyar Minjibir Journalist Forum

Date:

Minjibir Journalist Forum na mika sakon ta’aziyya da alhini ga daukacin al’ummar karamar hukumar Minjibir bisa rashin wasu jiga-jigan al’umma da suka rasu a ‘yan kwanakin nan.

Wadanda suka rasu sun hada da:

Marigayi Engr. Salisu Abdulwahab (Galadiman Tsakuwa) – Fitaccen dan kasa mai kishin al’ummarsa.

IMG 20250415 WA0003
Talla

Marigayiya Nasiba Sabo (Matar Isma’il Bello) – Uwar gida nagari da aka san ta da kyawawan halaye.

Dr. Bashir Aliyu Umar ya Sami Babban Mukami a Nigeria

Marigayi Alhaji Bala Zabainawa – Tsohon Sakataren Mulki na karamar hukumar Minjibir wanda ya bayar da gudunmawa wajen cigaban al’umma.

Marigayi Hon. Malam Saleh Ado Minjibir – Tsohon shugaban majalisar matasa, tsohon babban sakatare a gwamnatin jihar Kano kuma tsohon shugaban karamar hukumar Minjibir.

InShot 20250309 102403344

Marigayi Malam Sani Hamza Tsoho – Ma’aikaci a makarantar sakandaren ‘yan mata ta gwamnatin tarayya dake Minjibir, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen ilimantar da mata.

Muna addu’ar Allah ya gafarta musu, ya jikansu da rahama, ya basu Aljannah Firdausi. Haka kuma muna rokon Allah ya baiwa iyalansu, ‘yan uwa da daukacin al’ummar Minjibir hakurin jure wannan babban rashi.

Mai Sanarwa:
Hussaini Kabir Minjibir
Domin Minjibir Journalist Forum

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Abba Ya Sanya Hannu Kan Dokar Kafa Gaya Polytechnic

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanya...

Sojoji sun mikawa Tinubu Shawarwari yadda za a kawo karshen matsalar tsaron Nigeria

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya karɓi rahoton dakarun sojan...

Shugaba Tinubu ya sake nada Buba Marwa a matsayin shugaban NDLEA

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake tabbatar da nadin...

Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa Ya Koma Jam’iyyar APC a Hukumance

Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar...