Gwamnatin Kano ta shirya magance matsalar karancin gidaje a jihar – Kwamishinan gidaje

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Gwamnatin jihar Kano ta jaddada kudirinta na magance matsalolin karancin gidaje da suka addabi jihar .

Kwamishinan gidaje da raya birane na jihar, Arc. Ibrahim Yakubu Adamu, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da daraktocin ma’aikatar. Ya ce gwamnati na da kwarin gwiwa ga daraktocin wajen ganin ta kawo karshen kalubalen rashin gidaje a jihar.

IMG 20250415 WA0003
Talla

Arc Adamu, ya bayyana cewa a cikin wata biyu da kafa ma’aikatar ta samu damar gano wuraren da ake don gina gidaje da suka hadar da Lambu a karamar hukumar Tofa, Yargaya a karamar hukumar D/Kudu da kuma kammala ayyukan gina gidaje na garuruwan Kwankwasiyya, Amana da Bandirawo, kamar yadda gwamnan Abba Kabir Yusuf yake fata.

A wata sanarwa da daraktan wayar da kan al’umma na ma’aikatar Adamu Abdullahi ya aikowa Kadaura24, ya ce Kwamishinan ya kara da cewa ma’aikatar za ta himmatu tare da bullo da wasu tsare-tsare na gidaje don bunkasa Birane da karkara.

Dr. Bashir Aliyu Umar ya Sami Babban Mukami a Nigeria

Don haka, Kwamishinan, ya shawarci Shugabannin ma’aikatar da su duk abun da ya dace don cimma burin ciyar da jihar gaba kamar yadda gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta da a gaba .

InShot 20250309 102403344

Don haka Kwamishinan ya yi kira ga Daraktocin da su sake jajircewa wajen kawo sauyi a jihar. Ya kara da cewa sabuwar ma’aikatar gidaje da raya birane ta kuduri aniyar ganin kowane dan Kano ya samu gida mai sauki da inganci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Abba Ya Sanya Hannu Kan Dokar Kafa Gaya Polytechnic

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanya...

Sojoji sun mikawa Tinubu Shawarwari yadda za a kawo karshen matsalar tsaron Nigeria

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya karɓi rahoton dakarun sojan...

Shugaba Tinubu ya sake nada Buba Marwa a matsayin shugaban NDLEA

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake tabbatar da nadin...

Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa Ya Koma Jam’iyyar APC a Hukumance

Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar...