Ku rika sanya kishin Kano da mutuncinta a maganganunku – Gwamnan Kano ya fadawa Sojojin baka

Date:

Daga Isa Ahmad Getso

 

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi bukaci masu gabatar da shirye-shiryen siyasa a gidajen radio da sojojin baka da su rika fifita kishin jihar Kano, su kuma su zamo masu kare mutunci, hadin kai da addini a cikin maganganun da suke a gidajen radio.

Gwamnan ya yi wannan kiran ne a yayin rufe taron bitar yini biyu da ma’aikatar yada labarai da harkokin cikin gida ta jihar Kano tare da hadin gwiwar hukumar dake kula da gidajen Radio da Talabijin ta kasa NBC ta shirya wa masu gabatar da shirye-shiryen siyasa da sojojin baka.

Gwamna Yusuf wanda ya samu wakilcin sakataren gwamnatin jiha Alhaji Umar Farouk Ibrahim ya yaba da wannan shiri na hada kan masu magana a kafafen yada labarai daga sassa daban-daban, tare da bayyana gagarumin rawar da su ke takawa wajen fadakar da al’umma al’amuran da ke faruwa a kasa .

IMG 20250415 WA0003
Talla

Ya kuma jaddada alhakin da ya rataya a wuyan duk masu ruwa da tsaki da suka hada da iyaye da sarakuna da shugabannin al’umma da malamai da ’yan kishin Kano da su hada kai don kare martabar jihar da inganta dabi’un da ke karfafa hadin kan al’umma da kuma hakuri da juna.

Gwamnan ya kuma nuna jin dadinsa ga kungiyar ta Gauta Club bisa karramawar da ta yi ma sa, inda ya bayyana hakan a matsayin wani abin karfafa gwiwa wajen samar da shugabanci na gari da hada kan al’umma.

Yadda Ganduje ya karbi Kawu Sumaila, Rurum, Baffa Bichi, Rogo da wasu bayan ficewarsu daga NNPP

Da yake jawabi a wajen taron, Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya yaba wa mahalarta taron bisa yadda suke ba shi hadin kai, wanda ya taimaka wajen samun nasarar taron.

Ya kuma gargade su da kada su bari a yi amfani da su wajen bata sunan wasu a kafafen yada labarai, yana mai gargadin cewa hakan na iya haifar musu da gagarumar matsala.

 

Kwamared Waiya ya jaddada mahimmancin mutunta juna da sanin makamar aiki a tsakanin masu magana kan harkokin siyasa, ba tare da la’akari da banbancin jam’iyya ba, ya kuma jaddada aniyar ma’aikatar wajen tabbatar da kyawawan halaye da wayar da kan jama’a.

Kwamishinan ya kuma nuna godiya ga Gwamna Yusuf bisa amincewarsa da goyon bayansa wajen samun nasarar gudanar da taron bitar.

InShot 20250309 102403344

A yayin taron, an gabatar da makalolu da kasidu da dama, yayin da kuma kungiyar ta Gauta Club ta ba Gwamna Abba Kabir Yusuf lambar yabo ta 2025 don karramawa da irin sadaukarwar da yake yi wajen ci gaban jihar Kano.

Kungiyar ta Gauta ta kuma bayar da lambar yabo ga kwamishina Waiya bisa yadda ya farfado da kungiyar da kuma nuna godiyarsa ga jagoranci da hidimar da yake yi a jihar.

A wata sanarwa da daraktan aiyuka na musamman na ma’aikatar yaɗa labarai ta jihar Kano Sani Abba Yola ya aikowa Kadaura24 ya ce a karshen taron kwamishinan ya gabatar da takardar shedar halartar taron ga dukkan mahalarta taron.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da gudu zan karɓi tayin kujerar mataimakin shugaban ƙasa – Barau Jibrin

Daga Isa Ahmad Getso Mataimakin shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata...

Inganta tsaro: Shugaban K/H Tarauni ya ba da fili domin gina ofishin Civil Defence a karkasara

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Shugaban karamar hukumar Tarauni, Alhaji Ahmed...

Gwamnan Kano ya yi sabbin nade-nade

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya nada Malam...

Gwamnatin Kano ta bada hutun sabuwar shekarar Musulunci

Gwamnatin Jihar Kano ta ayyana gobe Alhamis, 26 ga...