Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Dan majalisar dattawa daga Kano ta Kudu Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila ya tabbatar da ficewarsa daga jam’iyar NNPP zuwa APC.
Kawu Sumaila ya tabbatar da haka ne a shafinsa na Facebook.

Yace eh , gaskiya ne jita jitar da ake yadawa cewa na fice daga jam’iyar NNPP zuwa APC,kuma nayi hakan ne domin samar da jin dadi da walwalar al’ummar da nake wakilta.
Idan za a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito Kawu Sumaila shi da wasu yan majalisar wakilai da ake zargin sun raba gari da gwamnatin kano suka gana da Shugaban jam’iyar APC na kasa Abdullahi Ganduje a Abuja.
Yan majalisar sun hada Hon. Kabiru Alassan Rurum da Ali Madakin Gini da Abdullahi Sani Rogo
Sai dai su yan majalisar ba su sanar da komawa APC ba har Yanzu