Shugaban Hukumar tace fina-finai da Dab’i ta Jahar Kano Alh. Abba El-mustapha ya aike da jami’an Hukumarsa kan manyan titinan Jahar Kano domin sa ido ga matuka baburan adai-daita sahu tare da kama duk wani baburin na adai-daita sahu da aka samu sanye da hotunan batsa ko rubuta kalaman da ba su yi daidai da tarbiya ba.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar Abdullahi Sani Sulaiman ya sanyawa hannu kuma aka aikowa Kadaura24.

Abba El-mustapha ya ce wannan na daga cikin aiyukan da ya rataya a wuyan Hukumar na tabbatar da anyi hoto mai tsafta tare da lika shi a inda ya dace, sannan kuma aikin hukumar ne ta tantance duk wani rubutu kafin ya isa ga idanun a’lummar Jahar Kano.
Yanzu-yanzu: Ganduje ya magantu kan batun komawar Kwankwaso APC
A ya yin da yake gudanar da aikin, Daraktan Dab’i na Hukumar Alh. Abubakar Zakari Garun Babba ya bayyana dangane da yadda ya ga wasu daga cikin matuka baburan adai-daita sahu ke lika hotunan da basu dace ba tare da rubuce rubuce marasa ma’ana wanda yace Hukumar bizata cigaba da lamintar yin hakan ba a fadin Jahar Kano.
A karshen ya yi kira ga matuka baburan na adai-daita sahu da su guji aikata duk wani laifi da zai jamisu fushin Hukumar. Abubakar Zakari ya kuma kara yin kira garesu ta sauran al’umma da su bawa Hukumar hadin Kai tare da goyan baya domin cigaban Jahar Kano.