Majalisar dokokin jihar Kano ta nemi al’ummar jihar Kano su yi watsi da rahoton da freedom Radio ta yi game da aiyukan yan majalisar a shekarar 2024 .
Kadaura24 ta rawaito Freedom Radio dai a wannan ranar ta litinin ne ta fitar da rahoto kan kididdigar yadda kowanne dan majalisar ya gabatar da kudirori a zauren majalisar cikin shekarar 2024.

Rahotan ya nuna cewa shugaban majalisar Hon. Jibrin Isma’il Falgore da wasu yan majalisu ba su gabatar da kudiri ko daya a shekarar da ta gabata ba.
Da yake ganawa da manema labarai Daraktan yada labaran majalisar Kamaludden Sani Shawai, ya ce rahoton na freedom Radio ba shi da tushe ballantana makama.
2027: Shugabannin APC a Kano ta Kudu sun mika bukatarsu ga Sanata Kawu Sumaila
” Akwai kura-kurai da rashin sanin aiyukan yan majalisar a cikin rahoton na Freedom Radio, don haka muna kira ga al’ummar jihar Kano da makwabtan jihar da su yi watsi da rahoton”.
Game da shugaban majalisar da rahoton Freedom Radio ya nuna cewa bai gabatar da ko kudiri daya a shekarar 2024, Kamaludden ya ce dama baya daga cikin aiki shugaban majalisar gabatar da kudiri.
Shawai ya nuna cewa ai Shugaban Majalisa ya yi kokari matuka a shekarar 2024 wajen jagorantar dukkan zaman da majalisar dokokin jihar ke yi, da sauran ayyukan da aka dorawa Shugaban.
Sai dai Freedom Radio ta ce tana nan akan bakanta na wancan rahoto wanda ya kunshi gaskiya da gaskiya wanda kuma tushensa ya fito ne daga ita Majalisar.
Freedom Radio ta kuma ba da tabbacin za ta yi fashin akan lamarin a labaranta na karfe 7 na yammacin ranar litinin.