Kisan Gilla: Muhimman abubuwan da Gwamnatin Kano ta gabatar wa gwamnatin Edo

Date:

Hukumomi a jihar Kano, sun yi ƙarin haske game da bayanai da sunayen da aka tattara na iyalan mutanen da aka kashe a garin Uromi, da suka miƙa wa gwamnatin jihar Edo.

Tun da farko gwamnatin jihar ta Kano ta kafa kwamiti da zai gudanar da bincike tare da tattara bayanan iyalan mafarautan da aka kashe.

Mataimakin gwamnan jihar Kano Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo da ke jagorantar kwamtin da ya miƙa bayanan ga gwamnan jihar Edon ya ce sun ziyarci mutanen su, a idan lamarin ya faru, da shugabanin yankin kan lamarin.

FB IMG 1744283415267
Talla

“Mun gana da shugabanin na siyasa, sarakuna da na Addinai na wurin, mun kuma gamsu da Matakan da gwamantin ta Edo ta dauka kan lamarin,” in ji mataimakin gwamnan na Kano.

Haka kuma ya ce gwamnatin jihar tuni ta dauki wasu matakai da suka hada da kama wadan ake zargin suna da hannu a lamarin, haka kuma an rushe kungiyar yan sakai ta Vigilante, da ake zargi da hannu a kisan mafarautan, sannan hukumomin tsaro na yan sanda da na DSS na ci gaba da neman sauran wadan ake zargin suna da hannu a lamarin.

Yadda za mu koyawa Matasa 5000 Noman zamani – Shugaban hukumar raya kogunan Hadeja-Jama’are

Kwamaret Aminu Abdulsalam Gwarzo ya kuma ce ‘sun tabbatar mana da kama mutum 14, sannan akwai ƙarin wasu mutane da ake ci gaba da nema’, a cewar sa.

Haka kuma ya ce cikin bayanan da suka mikawa gwamantin ta Edo sun hada da na ‘mutum bakwai daga cikin wadan da suka rasu sun futo da karamar hukumar Bunkure, sai biya zuwa shida daga Kibiya, sai daya daga Rano, da Garko da daya daga Dawakin Kudu, an tantance su wa nene su, da makusantansu, ko masu kula da su, da bayani na baka na wadan da suka tsallake rijiya da baya.

‘Mun yi da wajewa da shi cewar za a biya yan uwan wadan da aka halaka diyya, kuma ya yi mana alkawarin cewar za su duba rahoton, za kuma su yi abin da ya kamata akai, haka kuma kasan akwai wadan su kuma dukiyoyinsu suka salwanta, sakamakon far musun da aka yi, mun kuma mika masa rahoton mu, da muka tattara’, in ji Kwamaret Aminu Abdulsalam Gwarzo.

InShot 20250309 102403344

A nasa bangaren gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo ya ce Shugaba Tinubu bai ji daɗin abin da ya faru ba na kisan matafiyan a Uromi, kuma a shirye yake ya bi diddigin lamarin domin magance kare sake aukuwar lamarin.

“Ina tabbatar muku cewa gwamnatin tarayya da ta Edo sun kafa kwamitin bincike domin gano haƙiƙanin abin da ya faru domin magance matsalar baki ɗaya.

“Wannan rahoton da kuka kawo mana zai taimaka wajen sauƙaƙa mana bincike, don haka kada ku damu. Za mu yi abin da ya dace, kuma za mu fitar da sakamakon binciken domin kowa ya gani.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano za ta inganta walwala ma’aikatan dake kula da harkokin kudi – Babbar Akanta

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Gwamnatin jihar Kano ta ce za...

Fadar Shugaban Kasa ta magantu kan allunan tallan Tinubu da suka mamaye Abuja da Kano

Fadar shugaban Najeriya ta nesanta kanta daga wasu allunan...

Yansanda sun kama mafarauta huɗu ƴan asalin Jihar Kano a Edo

Rundunar yansanda ta kasa reshen jihar Edo ta tabbatar...

Kotu a Amurka ta umurci FBI da hukumomin yaƙi da ƙwayoyi su saki bayanan bincike kan Tinubu

  Kotun Ƙoli ta Ƙasa ta Washington D.C. a Amurka...