Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana ranar Lahadi 6 ga Afrilu, 2025 a matsayin ranar komawa makaranta ga ɗaliban makarantun kwana na gwamnati da masu zaman kansu, a matakin firamare da sakandare, domin cigaba da zangon karatu na uku na shekarar 2024/2025.
Yayin da ɗalibai a makarantun jeka Ka dawo a faɗin jihar za su koma makaranta a ranar Litinin 7 ga Afrilu, 2025.
Dambarwar Rivers: AIG Gumel ya gamu da fushin Sufeto Janar na yan sandan Nigeria
Wata sanarwa daga Daraktan Wayar da Kai na Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano, Balarabe Abdullahi Kiru, ya bukaci iyaye da masu kula da ɗalibai da su lura da ranar komawar makaranta domin tabbatar da bin wannan umarni gaba ɗaya.

Sanarwar ta ambato Kwamishinan Ilimi, Dr. Ali Haruna Makoda, yana jaddada cewa za a ɗauki matakin ladabtarwa ga duk wani ɗalibi ko ɗaliba da ya ƙi bin wannan umarni.
Ya shawarci ɗalibai da su guji kawo haramtattun abubuwa irin su wuka, reza ko miyagun ƙwayoyi zuwa makaranta, tare da zama masu bin doka domin samun nasara a karatunsu.