Daga Isa Ahmad Getso
Babban Sufeton ‘yan sandan Nigeria, Kayode Egbetokun, ya mayar da Mataimakinsa da ke kula da Yankin Zone 7 Abuja, Usaini Gumel, zuwa Sashen Hulɗa da Jama’a, Bincike da Tsare-tsare, bisa zargin cewa ya bayyana ayyana dokar ta-ɓaci a jihar Rivers da kuma dakatar da Gwamna Sim Fubara a matsayin abin da ya saɓawa kundin tsarin mulki.
Rahotanni sun bayyana cewa Mista Gumel ya faɗi ra’ayinsa kan dokar ta-ɓaci ne a cikin ofishinsa yayin wata tattaunawa da wasu daga cikin abokan aikinsa, amma ɗaya daga cikinsu ya tona masa asiri ya kai rahoto ga babban Sufeto Janar.

AIG Gumel, wanda ya fara aiki a Zone 7 Abuja a ranar 19 ga watan Fabrairu, bai samu wata takardar tuhuma ko gayyata don kare kansa a hukumance ba kafin a tura shi zuwa sabon sashen.
Gwamnan Kano ya bayyana dalilin da yasa ya sake dawo da Sarkin Gaya
Yayin da Zone 7, wacce ke kula da Babban Birnin Tarayya da Jihar Neja, ke da matakin aiki mai muhimmanci da kuma ɗaukaka, ana kallon Sashen Hulɗa da Jama’a, Bincike da Tsare-tsare a matsayin wuri na ladabtarwa.