Fitaccen jarumi a Masana’antar Kannywood Sadik Sani Sadik ya ce shi ba fadakarwa ya ke yi a fim ba, inda ya ce neman kuɗi kawai ya ke yi.
Jarumin ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da Gidan Rediyon Freedom, inda a ciki yake cewa ba tarbiyya yake koyarwa ba, ballantana a ce yana bata tarbiyyar.
A cewarsa, “Ni ban ce ina fadakarwa ba. Ni Sadik Sani Sadik ban ce ina fadakarwa ba. Ban ce ina tarbiyyantarwa ba.

Tarbiyya ana ba yaro daga gida ne, fadawarka kuma malamai ne ke yi. Ni ba mai fadakarwa ba ne. Ni mai neman kudi na ke.
“Shi fim ba shi da yare, ba shi da addini, saboda haka ya danganta da yanayin da za ka gudanar da fim dinka.
“Idan danka ya kalli fim dina, tarbiyyarsa ta tabu, ba daga ni ba ne, daga kai ne. Idan ma danka bai kalli fim din Hausa ba, zai kalli na Indiya da wakokin Turawa da ake rungume-rungume.
Zargin Handama: Al’ummar Garin Danzaki Sun Nemi Agajin Gwamnan Kano
“Ni kuma a fim din Hausa idan na taba hannun mace ya zama abin magana, ban isa ba wallahi.”
Game da mata sun fi maza samun kudi, sai ya ce, “Wasu matan sun fi wasu mazan kudi.
“Kudi ai sirri ne ba wai ka ga mutum ya hau motoci ko ya sanya gwala-gwalai ba ne.
“Ya danganta ne, wani idan yana da dubu daya sai ka gane, wani kuma yana da miliyan daya, amma ba za ka gane ba.”