Daga Rahama Umar Kwaru
Babban Daraktan Hukumar Samar da Wutar Lantarki ta Karkara (REA), Engr. Abba Ganduje, ya jaddada kudirin hukumar na tallafawa shirin samar da makamashi na jihar Kano .
Abba Ganduje ya bayyana hakan ne yayin da ya karbi bakuncin wata babbar tawaga daga gwamnatin jihar a Abuja.
Tawagar karkashin jagorancin manyan jami’an gwamnatin Kano, ta ziyarci REA ne domin tattaunawa kan dabarun fadada ayyukan samar da makamashi don inganta wutar lantarki a muhimman bangarorin da suka hada da kiwon lafiya, ilimi, noma, al’ummar karkara, da sauransu.

Da yake maraba da tawagar, Engr. Abba Ganduje ya jaddada kudirin hukumar REA na karfafa hadin gwiwa da gwamnatin jihar Kano don tabbatar da dorewar hanyoyin samar da makamashi da za su inganta ayyukan yi da bunkasar tattalin arzikin jihar da na kasa baki daya.
“Mun kuduri aniyar yin aiki kafada da kafada da gwamnatin jihar Kano domin aiwatar da ayyukan makamashi masu inganci wadanda za su canza muhimman sassa da inganta rayuwar al’ummar jihar Kano,” in ji shi.
Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci
Tawagar ta Kano ta hada da kwamishinonin ilimi, sufuri, da raya karkara da al’umma, tare da manajan daraktocin hukumar samar da wutar lantarki ta karkara (REB) da KanInvest.
Haka kuma akwai mai ba gwamna shawara na musamman kan harkokin kiwon lafiya wanda kuma shi ne likitan gwamna Dr. Ibrahim Musa.
Bayan shekaru 20, Kotun Ƙoli ta sanya ranar yanke hukunci kan rikicin masarautar Gwandu
A yayin ganawar, bangarorin biyu sun yi nazari kan hanyoyin yin hadin gwiwa da juna, inda su ka nuna muhimmancin samar da makamashi wajen bunkasawa da tabbatar da ingantaccen wutar lantarki ga cibiyoyin gwamnati da na kauyuka na Kano.
Taron ya nuna wani muhimmin mataki a yunkurin samar da makamashi na jihar Kano, Sannan hukumar REA ta yi yin duk mai yiwuwa don inganta harkokin makamashi a Kano don cigaban jihar .
Tawagar da gwamna Abba Kabir Yusuf ya aike ta samu jagorancin kwamishinan lantarki da makamashi Engr. Dr. Gaddafi Sani Shehu.