Daga Aminu Gama
Kotun shari’ar musulunci da ke zamanta a fagge yan alluna a jihar Kano ta aike wani magidanci da ake zargi da ikirarin bin mamata bashi zuwa gidan gyaran hali.
Mai shari’ar Umar lawan Abubakar na kotu mai lamba 1 a unguwar fagge yan Alluna ne ya bayar da umarnin garkame mutumin har zuwa ranar 14 ga watan 04 2025 domin cigaba da sauraren karar.
Tun da farko lauyan Gwamnati Zaharaddini Mustapha ne ya karantawa wanda ake kara tuhumar da ake yi masa.

Ana dai tuhumar mutumin ne da zargin zuwa gidajen da aka yi mutuwa inda yake karyar cewa yana bin wanda ta rasu kudi.
An dai kama mutumin ne yayin da ya je gidan su wani mamacin mai suna Yusuf Mansur Ashura inda ya yi da’awar yana bin mamacin kudi Naira dubu dari uku sakamakon kasuwancin Doya da suka yi.
Sai dai da aka zurfafa bincike sai aka gano mutumin karya yake yi, saboda an sami akalla mutane uku a gidan mutuwar da suka ce sun gane shi, domin mutumin ya taba zuwa ya ce yana bin mamatansu kudade.
Yanzu-yanzu: Manjo Hamza Al-Mustapha ya koma jam’iyyar SDP
Daga nan ne aka mika shi ofishinsa yansanda inda su kuma suna kawo shi kotu don ya girbi abun da ya shuka.
Tuni dai wanda ake kara ya amsa laifinsa kuma ya roki mai shari’ar da yayi masa sassauci.