Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana cewa akwai bukatar kebe wata rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a jihar Kano.
Kwamishinan ya bayyana haka ne a lokacin da mambobin kungiyar tsofaffin daliban makarantar Dawakin Tofa Science Secondary School, yan aji na1991, da su ka kai masa ziyara ofishinsa.
Kwamared Waiya wanda shi ma mamba ne a kungiyar ya bayyana cewa kafa irin wannan rana zai kara dankon zumunci a tsakanin tsofaffin dalibai da kuma bayar da damammaki na sake haduwa da abokan da aka dade ba a hadu da su.tantance halin da tsofaffin daliban ke ciki domin bayar da tallafin da ya .

Ya kuma nuna jin dadinsa bisa yadda ga tsofaffin ‘yan ajinsu suka ziyarce shi, inda ya bayyana irin rawar da kungiyoyin tsofaffin daliban ke takawa wajen ci gaban makarantun da suka gama.
A nasa jawabin, shugaban kungiyar tsofaffin daliban Dawakin Tofa Science Secondary School ’91 Comrade Inuwa Ishaq Inuwa, ya bayyana cewa sun kai ziyarar ne domin taya Kwamared Waiya murnar nadin da aka yi masa a matsayin kwamishina.
Yanzu-yanzu: Manjo Hamza Al-Mustapha ya koma jam’iyyar SDP
Kwamared Ishaq ya bayyana cewa kungiyar ta su ta kunshi kwararru daga bangarori daban-daban da suka hada da jami’an tsaro, farfesoshi, da manyan jami’an gwamnati.
Ya kuma yabawa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa nada mamban su a matsayin kwamishina a ma’aikatar yada labarai da harkokin cikin gida.
Ya yi addu’ar Allah ya yi masa jagora da nasara ga Kwamishinan a matsayinsa na jagoranci.
Shugabannin kungiyar da suka raka shugaban ziyarar sun hada da Sakataren kungiyar Alh. Hasan Umar Kazaure, Alh. Abas Sa’idu Kiru, Alh. Sani Garba Kachako da wasu mambobi biyu na kwamitin amintattu na kungiyar Alh. Adamu Ibrahim Dabo Dawakin Tofa da Alh. Auwalu S. Mu’azu.
Bayan kammala ziyarar, shugaban kungiyar ya mika lambar yabo ta musamman ga kwamishinan a matsayin alamar karramawa a madadin daliban aji na 91.