Hukumar Shari’ah ta jihar Kano karkashin jagorancin mukaddashin shugabanta Sheikh Malam Ali Dan Abba a yau Laraba ya jagorancin taron kaddamar da kamitocin da zasu dauki gabarar kawo sauyi a jihar Kano kan abin da ya shafi shari’ar Musulunci a jihar.
Dan Abba yayi maraba da manyan baki da hukumar ta gayyata kuma suka sami damar halartar zaman, manyan bakin da suka sami damar zuwa sun hada da Barr Mujiburrahman tsohon shugaban kungiyar lauyoyi ta jihar (Ungoggo Branch Kano) kuma tsohon shugaban kungiyar lauyoyi Musulmi ta Kano, Kano sai Baba Jibo Ibrahim mai magana da yawun kotuna ta jihar Kano sai wakilin shugaban gidajen gyaran hali da tarbiyya ta Kano sai wakilin kwamishinan yan sandan jahar Kano DSP Abdullahi Haruna kiyawa da sauran mambobi na hukumar da manyan limamai.
Daga bisani Mal Dan Abba ya fadi makasudin wannan zama da samar da wadannan kwamiticin, wanda yace babban kalubalen da zamu fara sawa a gaba shine Sulhu kamar yadda shugaba sallahu Alaihi Wasallama yayi, sannan iyaye su saka ya’yan su a gaba wajen tsaida sallah, domin tsaida sallah shine babban jigon magancewar wadannan matsalolin da aka ciki a wannan jihar na shaye-shaye, kwacen waya, tabarbarewar tarbiyya raba da yawan cinkoso a gidajen gyaran hali, matsalolin aure da sauran matsaloli da ake fuskanta, in da ya tabbatar da faɗin Allah na cewar tsaida sallah na hana alfasha da sauran miyagun ayyuka. “Allah ya karfafi Sulhu don haka muma zamu bada karfi akansa sosai da sosai”.

Hakazalika yayi kira ga limamai da ladanai kan samun hadin kai idan dai Allah aka nufata, a karshe yayi fatan wadannan kwamitoci da aka samar na
-Da’awa
-Sulhu
-Tantance limamai da ladanai
-Bita da wayar da kan al’umma kan addini
Da fatan zasu kawo cigaba da hadin kan al’ummar jihar Kano dama kasa baki daya kamar yadda mai girma Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf yake da fata a garesu.
A karshe yayi kira ga al’umma da Iyaye wajen bada hadin kai da goyon baya, idan wata matsala ce kafin kuke ko ina ku zo wannan hukuma da izinin Allah za a warware ko wacce irin matsala cikin sauki.
A nasa bangaren shugaban kungiyar lauyoyi ta jihar Kano Barasta Mujiburrahman yace yaji dadin wannan gayyata da aka masa , kuma a saninsa tun daga lokacin Malam Ibrahim Shekarau ba a taba wata gwamnati a jihar nan da take kokarin habaka Shari’a ba sai wannan gwamnatin ba.
A baya mun yi irin wannan kokarin kafa kwamitin Sulhu a kananan hukumomi lokacin Malam Yahaya Farouk Chadi a lokacin ina sakatare na hukumar Hisba wanda a gaskiya anyi ayyukan sulhu kala kala wanda da Allah yasa an cigaba da wannan tsarin da ba haka muke ba yanzu da Kano ta wuce haka.
Yayi kuma kira ga gwamnan Kano kan inganta wannan hukuma ta Shari’a kamar yadda take a baya da sauran hukumomin addini na Kano.
Yayi kuma kira da Allah ya kawowa Kano zaman lafiya da ci gaba mai dorewa.

Shi ma Baba Jibo Ibrahim ya yaba da wannan gayyatar da aka musu kuma ya tabbatar da cewar kwamatin sulhu da aka yi a cikin wadannan kwamiticin zai taimaka wa bangaren sharia a jihar gaya, kuma yayi alƙawarin cewar hukumar kotuna ta jihar Kano zata shigo cikin wannan kwamiti don tabbatar da wannan kwamiti wanda duk sulhun da aka yi hukumar kotuna zata buga tambari wanda ya zama doka kenan, maganin masu ganin cewar kwamitin bashi da hurumin tursasawa ko masu taurin kai.
Shima babban daraktan gidan Dr Sani Ashir ya nuna farin cikinsa da godiya ga Allah yadda Manyan baki suka amsa kiran nasu, kuma yayi kira ga yan kwamati da aka daura wa nauyin da su dubi Allah wajen gudanar da wannan aikin da Allah ya dora musu.
Shima gwani Hadi Kwamishina na ɗaya a hukumar ya godewa Allah ya kuma yi kira da al’ummar jihar Kano da su zamo ababen koyi da alfahari da su a ko ina haka zalika yayi kira ga malamai akan su guji nitso a cikin daudar duniya.
Karshe dai taro ya tashi cikin jin dadi da annashuwa
Da kuma rokon Allah ya tabbatar da nasarorin da ake nema.
Sunayen Yan kwamatin
Kwamatin sulhu
1.Ibrahim Inuwa (Limamin Ja’en) Chairman
2. Ibrahim Lawan Karaye DPRS Vice Chairman
3. Aliyu Umar kibiya (Limamin Kibiya) Member
4. Nana Aisha Muhammad ACEO Member
5. Legal Adviser Member
6. Abubakar I. Sulaiman PEO Secretary
Kwamatin DA’AWA
1. Kabiru Na’ibi Karaye Board Member Chairman
2. Muhammad Abu Musa DIP Vice Chairman
3. Nasiru Aliyu Harazimi Board Member Member
4. Abubakar Sani Madatai Board Member Member
5.Yawale Sulaiman Gulu Board Member Member
6. Zainab Sani Matori Member
7.Hamisu Murtala Gwarzo Secretary
Kwamatin Tantance limamai da ladanai
1. Muh’d Mukhtar Mama Darma Board Member Chairman
2. Yusha’u Abdullahi Bichi DIE Vice Chairman
3. Muhammad Abu Musa DIP Member
4. Naziru Saminu Dorayi Board Member Member
5. Adamu Ibrahim Member
6. Adnan Nasir Koki Secretary
Kwamatin Bita da wayar da kan al’umma kan addini
1.Malam Abubabakar Sharif Bala Board Member Chairman
2. Sani Zarewa DSD Vice Chairman
3. Mahbub Sarki DISA Member
4. Abdullahi Hassan Member
5. Balarabe Aliyu Member
6.Maryam Lawan Member
7. Sani Musa Muhammad Secretary
Da hannun
Musa A Ibrahim (Best Seller)
Mukaddashin P R O