Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Rundunar yansanda ta kasa reshen jihar Kano ta ce ta sami nasarar kama wasu yan bindiga da suka shigo jihar Kano.
Kadaura24 ta rawaito Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na Rundunar yansanda ta Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar.

Ga abun da ya rubuta:
Jama’a Assalamu Alaikum!
Mun samu nasarar kama wadansu Yan Bindiga da sukai kutse zuwa Jihar Kano.
Zaku ji mu Insha Allah.
Ya ce Nan gaba kadan za su fito da karin bayani bisa nasarar kama yan bindigar.