Sabon Rikici ya Barke Tsakanin Jiga Jigan NNPP Kwankwasiyya a Kano

Date:

Daga Maryam Muhammad Ibrahim

 

Rikicin cikin gida ya sake barkewa tsakanin mai magana da yawun gwamnan jihar Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa da dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Dawakin Tofa, Tofa da Rimin Gado Tijjani Abdulkadir Jobe.

A Wani Saƙo da mai magana da yawun Gwamna Abba Kabir Yusuf Sanusi Bature D-Tofa ya wallafa a shafinsa na Facebook ya ce Mutuncin jobe a wajen sa shi ne ya yiwa mutane abinda ya kamata, tun da akwai hakkin su a hannun sa, Bature ya kara da cewa wallahi duk mutumin da mutane suka zaba to dolen sa ne ya sauke nauyin dake kansa.

InShot 20250115 195118875
Talla

Sanusi Bature ya yi togaciya da cewa “Kada wani ya dauka wai ko ina son takara saboda haka zan juri wulakanci, ni dan halak ne, kuma na yadda da kaddara wallahi ya fi komai sauki in hakura da takarar wajen kare mutuncin al’ummar mu”.

“Ya ƙara da cewa Takarar me? Kaine ka dauka sai da ita zaka rayu sai in fasa takarar kuma in yake ka tunda baka da shirin chanja hali”. A cewar Sanusi Bature

Fyade: Kotu ta yankewa wasu mutane 3 hukuncin kisa da yanke musu Mazakuta

Dama dai an jima ana zargin cewa Sanusi Bature na zawarcin waccen kujera ya Jobe ,shi ne ya sa suke ta samun tsamin dangantaka tsakaninsa da ɗan majalisar tarayya mai wakiltar rimin gado dawakin tofa rimin gado da tofa Tijjani Abduƙadir Jobe.

Ko a baya baya an hangi wani fefen video da ɗan majalisar ke kokawa tare da zargin cewa Baturen na yi masa zakon ƙasa sai gashi a wanan karan Bature ya fito fili ya bayyana dalilin rashin gamsuwa da salon wakilcin na Jobe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...