Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Kamfanin mai na kasa NNPC ya sake rage farashin man fetur a Nigeria.
A baya dai ana sayar da man fetur din ne a gidajen man NNPC akan N965 amma yanzu farashin ya koma N860 kowacce lita.
Sai dai har yanzu kamfanin NNPC bai sanar da ragin a hukumance ba , amma dai majiyar kadaura24 ta Punch ta tabbatar da cewa an rage farashin a wasu gidajen mai dake jihar Lagos.
Duk Kokarin da majiyar ta mu ta yi na jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na kamfanin ya ci tura.

Sai dai mataimakin shugaban kungiyar dillalan man fetur na kasa Hammed Fashola ya tabbatar da rage farashin man na kamfanin NNPC.
Shugaba Tinubu ya naɗa sabon shugaban NYSC
” Gaskiya ne NNPC ta fara sayar da mai akan N860 a gidajen mai, duk da cewar har yanzu ba su sanar da jama’a na, amma dai ni sun kirawo ni sun kuma fada min cewa za su yi wasu yan sauye-sauye.
Idan za a iya tunawa Kadaura24 ta a makon da ya gabata ne matatar man Dangote ta rage farashin man na kamfanin zuwa N845 kowacce lita.