Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Kasar Saudiyya ta sanar da ganin jinjirin watan Ramadan na Shekarar 1446 Bayan Hijra a Yau Din nan.
Kadaura24 ta rawaito, za a fara Azumin bana a kasa mai tsarki daga gobe asabar, a matsayin 1 ga watan Ramadana .

Kafar yada labarai ta Haramain Sharifain dake kasar Saudiyya ce ta Sanar da hakan a Sahihin shafinta na Facebook da X wato Twitter.
Ramadan: Sanata Barau ya bayar da tallafin kudi ga kungiyar Barau FC
Dama dai yau Juma’a ne 29 ga Watan sha’aban Kuma ita ranar da mai alfarma sarkin musulmi ya bada Umarnin a fara duban jinjirin watan duban wata a Nigeria.