Rundunar Yansandan Kano ta yi Karin Haske Kan Yunkurin Kone Gidan Sarki na Nasarawa

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Rundunar yansanda jihar Kano ta bayyana cewa matasan da su ka shirya yin zanga-zanga a ranar larabar da ta gabata so suka yi su farwa gidan Sarki na Nasarawa, inda Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero ya ke zaune.

” Rohotannin sirri da mu ka samu sun tabbatar mana da cewa matasan so su ka yi su fake da zanga-zanga sai su afkawa gidan Sarki na Nasarawa, hakan ta sa muka tarwatsa su kuma muka kama 17 daga cikin su”.

InShot 20250115 195118875
Talla

Kadaura24 ta rawaito mai magana da yawun rundunar yansanda ta jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels a ranar Alhamis da daddare.

Ya ce sun sami makamai wadanda su ka hadar da wukake da sauransu a hannun yaran da aka kama, kuma ya ce tuni suna sashin binciken manyan laifuka na rundunar yansanda dake Bompai Kano.

Bayan Rahoton Kadaura24, Gwamnan Kano ya dakatar da mai rikon mukamin shugaban ma’aikata

SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce “Bayanan sirri da muka samu ne yasa muka kara tsaurara tsaro wuraren masu muhimmanci kamar gidan Sarki Nasarawa inda Aminu Ado Bayero ya ke , sannan muka kara tsaro na gidan Sarki na cikin gari inda Muhammad Sanusi II yake zaune da gidan gwamnatin jihar Kano da dai sauran muhimman wurare”.

Da aka tambaye shin da gaske ne wadanda kuka ce kun kama dalibai ? Kiyawa sai ya kada baki ya ce duk cikinsu ba wani dalibi kamar yadda binciken farko ya nuna musu, ya ce hasali ma da makamai a jikinsu lokacin da muka kamasu.

Gwamnatin Kano ta bukaci Tinubu ya dauke Aminu Ado Bayero daga jihar

Ya ce da zarar sun kammala bincike za su mika wadanda aka kama din Kotu domin ta yi musu hukunci daidai da laifin da aka same su da shi.

SP Kiyawa ya kuma ba da tabbacin da zarar sun kammala bincike za su sanarwa al’umma sakamakon binciken kafin gurfanar da wadanda ake zargin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Ba za mu lamunci cin zarafi ko tozarta wasu da sunan Tashe ba – Hukumar Hisbah

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Hukumar Hisba ya jihar kano ta...

Da dumi-dumi: El-Rufa’i ya fice daga jam’iyyar APC

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya tabbatar da...

2027: Atiku Abubakar ya bayyana matsayarsa game da kasancewarsa a PDP

  Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya musanta rahotannin...

Cikakken Bayani Kan Yan Bindigar da Yansanda Su Ka Kama a Kano

Daga Rahama Umar Kwaru   Rundunar yansanda ta kasa reshen jihar...