Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya bayar da kyautar tallafin kudi ga yan wasa, masu horarwa, da shugabannin kungiyar kwallon kafa ta Barau FC.
Rabon tallafin kudin na zuwa ne, ya yin da ake shirin shiga azumin watan Ramadan, da Sanata Barau ya bayar da tallafin kudin domin karfafawa yan wasan kungiyar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na kungiyar Ahmad Hamisu Gwale ya sanyawa hannu kuma ya aikowa Kadaura24.

Sanata Barau, wanda ya sami wakilcin Kabiru Ado Lakwaya, mai taimaka masa kan harkokin matasa da wasanni, ya bayar da kyautar kudin ne a lokacin da ya ziyarci filin daukar horo na Kungiyar a ranar Juma’a a nan Kano.
Da dumi-dumi: Kotun Koli Ta Rushe Zaben Kananan Hukumomin Ribas
Kabiru Lakwaya ya ce wannan na daga cikin kokarin Sanata Barau Jibrin, na bayar da goyan baya ga yan wasa, da jamian kungiyar ta Barau FC.
A lokacin bayar da kyautar tallafin kudin, Kabiru Ado Lakwaya na tare da shugaban Barau FC Ibrahim Shitu Chanji, da Alhaji Abdul AP da Yahya Muhd da sauran masu ruwa da tsaki a kungiyar ta Barau FC.